Rabin Albashi: Muna Kokarin Shawo Kan Matsalar FG da ASUU, Gwamna Badaru

Rabin Albashi: Muna Kokarin Shawo Kan Matsalar FG da ASUU, Gwamna Badaru

  • Gwamna Muhammad Badaru na jihar Jigawa ya sanar da cewa shi da gwamnonin jihohi 35 na fadin kasar nan suna kokarin shawo kan matsalar FG da ASUU
  • Ya sanar da cewa shi da takwarorinsa zasu yi iyakar kokarinsu wurin tabbatar da cewa lakcarori basu sake fadawa wani yajin aikin ba
  • Gwamna Badaru ya sanar da cewa jama’a suna ganin cewa neman kujerar siyasa yana da wahala amma shugabancin yafi zama abun wahala

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Jigawa, Mohammad Abubakar Badaru, ya tabbatar da cewa gwamnonin jihohin 36 na fadin kasar nan suna yin duk abinda ya dace wurin shawo kan matsalar dake tsakanin kungiyar malamai masu koyarwa na jami’o’i, ASUU da gwamnatin tarayya kan albashinsu.

Gwamna Badaru
Rabin Albashi: Muna Kokarin Shawo Kan Matsalar FG da ASUU, Gwamna Badaru. Hoto daga vanguardngrnews.com
Asali: UGC

Gwamnan ya sanar da wannan ne yayin taron rantsar da sabbin shugabannin kungiyar daliban Najeriya da aka yi a Abuja ranar Alhamis, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Yi Alkawarin Karasa Aikin da Aka Yi Shekara 43 An Gaza Kammalawa a Arewa

Idan za a tuna ASUU ta fada yajin aiki tun watan Fabrairu har zuwa Oktoba, lamarin da ya gurgunta karatu a jami’o’i a fadin kasar nan.

Sun janye yajin aikin a ranar 14 ga watan Oktoba bayan kotun masana’antu ta umarcesu da su koma aji.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A farkon watan Nuwamba, gwamnatin tarayya ta biya malaman albashin rabin watan Oktoba, lamarin da ya fusata malaman.

Muna Kokarin Sasanci Tsakanin FG da ASU, Badaru

Amma Gwamna Badaru yace suna yin duk abinda ya dace wurin tabbatar da cewa lakcarorin basu dake fadawa yajin aiki ba.

Yace:

“A kan batun albashin rabin wata da aka biya mambobin ASUU, mu gwamnonin jihohi 36 tuni muka fara aiki kan hakan kuma da izinin Allah zamu shawo kan matsalar.
“Muna fatan ba za a sake shiga wani yajin aiki ba. Kun sha wahala daidai gwargwado. Kuma ina da tabbacin shugaban kasa ya san da hakan kuma muna duba duk wata halastacciyar hanya domin tabbatar da biyan albashin.”

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa Da Babban Na Hannun Damar Atiku, Wike Ya bayyana Matsayinsa na Karshe Kan Rikicin PDP

Jaridar Blueprint ta rahoto cewa, yayi alkawarin yin aiki da takwarorinsa na jihohi 35 domin tabbatar da cewa an inganta ilimi domin jin dadin dalibai.

“Zamu yi iyakar kokarin da zamu yi wurin daukaka kungiyar nan. Don haka ku tabbatar da cewa kuna da ni tare da takwarorina 35 na kasar nan saboda babu wanda a cikinsu ba zai so amsa kiran daliban Najeriya ba.
“Zamu goyi bayanku kuma mu tabbatar an samu cigaba a bangaren ilimi domin inganta bangaren dalibai.”

- Gwamnan yace.

Badaru ya kara da kira ga shugabannin NANS da su shugabanci kungiyar da tsoron Allah tare da saka jama’a a zukatansu inda yace:

“Idan muna yin zabe, muna jin cewa zaben shi ne abinda ya fi komai wahala amma shugabancin yafi wahala idan aka ci zaben.”

Shugaban NANs Ya Koka Kan Halin da Ilimi ya Shiga

A jawabin rantsuwarsa, sabon shugaban NANS, Kwamared Umar Barambu ya koka kan halin da bangaren ilimi ya shiga a kasar nan.

Kara karanta wannan

Mu ba Ma’aikatan Wucin-gadi Bane: Shugaban ASUU ya Wanke FG Tas

Yace:

“Kowacce gwamnati da ta san hakkinta ta san matsayin ilimi a bangaren cigabam kasa. Sai dai abun takaici, an yi watsi da wannan bangaren tun daga gwamnatocin baya.
“Halin da ilimi ya shiga a kasar nan ba lalacewa kadai bane, amma abin kunya ga kasar da take tunkaho na zama gagaruma a Afrika.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng