Mawaki Portable Ya Fusata Yayin da Ya Gano Masoyansa Sun Watsa Masa Kudaden Bogi
- Fitaccen mawakin nan na Najeriya, Portable ya bayyana a kafar sada zumunta domin caccakar wasu 'yan Najeriya da suka watsa masa kudin bogi a kulob
- Mawakin wanda ya bayyana zuwa birnin Fatakwal domin yin wasa a gidan kulob ya nuna bacin ransa ga abin da ya faru
- A bidiyon da Portable ya yada, ya nuna kudaden da aka watsa masa a kulob din, lamarin da ya dauki hankalin jama'a
Fitaccen mawaki a Najeriya, Habeeb Okikiola da aka fi sani da Portable ya sanya jama'a cece-kuce a kafar sada zumunta bayan da ya bayyana yadda wasu masoyansa suka watsa masa kasa a ido.
Mawakin ya fito ya bayyana cewa, wasu mutane a kulob sun yi masa yayyafin kudaden bogi yayin da yake tsaka da rawa da waka.
A wani bidiyon da ya yada a shafinsa, an ga mawakin na yaga wasu kudaden da yace na bogi ne tare da yiwa wadanda suka ba shi su tofin Allah-tsine.
Hakazalika, Portable ya ci gaba da caccakar masoyansa 'yan birnin Fatakwal saboda yadda suka bari aka ci masa fuska.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
An ji shi yana cewa, jama'ar Fatakwal basu nuna masa kauna ba.
Kalli bidiyon:
Martanin jama'a
@richie.richie127:
"Lallai fa, kudaden bogi."
@hon_armani25:
"Na tabbata yayin da kake ganinsu da damin 'yan 1k, ka kara kaimin rawa da waka, yi hakuri baba oloye."
@imindz_orf:
"Ka watsa na gaske sun watsa maka na bogi."
@topboi_rd:
"Mutumin ya yi sa bai gane na bogi bane tun a kan dandamali, Portable da ya gama dashi cikin gaggawa."
@official_kiski:
"Mama zeh na kirga kudaden bogi."
@cherry__x01:
"Sun cuce ka!! Ka watsa kudin gaske sun watsa maka na bogi ya kamata ka koyi darasi daga Fatakwal."
@aremo_hibee_dende:
"Ka watsa kudin gaske da yamma, yaran Fatakwal sun watsa maka na bogi da dare."
Ango ya hana a kira shi bayan 7 na dare jim kadan bayan shiga daga ciki
Wani ango kuma da ya samu wuri ya baje kolin halinsa, inda yace sam bai amince abokansa su sake kiransa ba bayan karfe 7 na dare.
Ya bayyana hakan ne a gaban kowa, inda ya gargadi jama'a da cewa su kula cikin raha.
Jama'ar da suka halarci auren sun yi dariya tare da taya shi murnar gama gauranta.
Asali: Legit.ng