Waye Mahaifin ki a Najeriya? ‘Yar TikTok Mai Shekaru 17 ta Siya Motar N20m

Waye Mahaifin ki a Najeriya? ‘Yar TikTok Mai Shekaru 17 ta Siya Motar N20m

  • Wata budurwa ‘yar Najeriya ma’abociya amfani da TikTok tayi suna bayan bidiyonta ya bayyana motar alfarmar da ta siya kirar Benz ta N20m
  • Wannan kuwa ya janyo maganganun mutane inda suka dinga tuhumarta kan yadda ta mallaki wannan motar mai tsada duk da karancin shekarunta
  • A yayin da wasu suke taya ta murna kan wannan nasarar rayuwa da ta samu, wasu sun dinga cewa ta cigaba da aikin da take in har halal ne

Wata matashiyar budurwa ‘yar Najeriya ma’abociya amfani da TikTok mai suna Shirin Borau a cikin kwanakin nan tayi suna baya ta bayyana cewa ta siya motarta ta farko tana da shekaru 17 a duniya.

Shirin
Waye Mahaifin ki a Najeriya? ‘Yar TikTok Mai Shekaru 17 ta Siya Motar N20m. Hoto daga TikTok/@shirinborua
Asali: UGC

Wannan nasarar da Shirin ta samu ya janyo maganganu a yanar gizo inda wasu suka dinga tuhumar yadda ta samu katafariyar motar nan a shekaru 17.

Wasu ma cewa suka yi matashiyar ba ita ta siya ba kawai fitaccen saurayinta mai wasan barkwanci, De-general ne ya siya mata.

Shirin wacce cike da murna ta wallafa a shafinta cewa ta siya Marsandi C300 2016, tana daya daga cikin mata masu TikTok dake samun cigaba a Najeriya inda take da mabiya 1.3m.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ga Bidiyon Shirin tana sanar da cigaba da ta samu:

Jama’a sun yi martani

@oluwa_martial_of_ibadan:

“Idan kin so ki siya Benz kina da shekaru 10, nima zan siya tawa.”

@official_godwin9:

“A Najeriya ba a bayar da lasisin tuki sai ka kai shekaru 18, me ke faruwa da wannan?”

@az_dives:

“Abun dariya, bana son ji daga baya cewa wani namiji ya siya mata kuma matarsa ta kwace. Daga nan sai su fara zagin juna a soshiyal midiya. Saboda kin ce da kudin TikTok ne ko?”

@ceejay2298:

“Amma kuma motar bata kai 20m ba ai ko… mu ma nan muna da mota ai.”

@cyruscasper007:

“Haka zaka ga masu bidiyoyin barkwancin nan, kwatsam wata daya za ka ga sun siya mota, yanzu kuma TikTok ne. Mene ne ke faruwa?”

@capt_joker:

“Shekaru 17? Kenan D-general yana soyayya da kananan yara?”

@gazzy_gnf:

“Idan ka yarda da duk abinda ka gani a TikTok kai ne wawa.”

Bidiyo: Matar aure ta bai wa mai kayan miya kyautar N1m, ta bayyana alherin da yayi mata a baya

A wani labari na daban, wata matar aure mai amfani da suna @abdulshally ta bai wa mutane mamaki da irin karamcinta tare da tuna alherinta.

Matar auren ta bayyana yadda ta nemi wani tsoho mai suna Shehule mai kayan miya inda ta gwangwaje shi da kyautar N1 miliyan saboda kyautatawa mahaifiyar ta da yayi a lokacin tana karama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel