UNICEF Zata Tallafawa Almajirai 2,764 A Jihar Kaduna Dan Ci-Gaba Da Karatun Firmare da Koyan Sana'oi

UNICEF Zata Tallafawa Almajirai 2,764 A Jihar Kaduna Dan Ci-Gaba Da Karatun Firmare da Koyan Sana'oi

  • Tun Lokacin Kullen Korona Gwamnatocin Jihohin Arewa suka Kaddamar Da maida almajirai Garuruwansu na asali
  • Ko a kwanannan Mai dai Shararen malamin addinin islama Sheik Dahiru Bauchi yayi ikirarin cewa akwai almajirai a Nigeria sama da dubu 100
  • Lokacin Mulkin Shugaba Jonathan, Gwamnatin sa ta fidda wani tsari na tallafawa almajirai da kula da su

Kaduna: Gwamnatin Jihar Kaduna tare da hadin gwiwar Asusun Kula da Ilimin Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) a ranar Laraba, sun kaddamar da rabon kudade ga yaran Almajirai a karkashin shirin ‘Children Street Programme’.

A karkashin shirin, Almajirai 2,674 da aka maida su ga iyaytensu ne, za su karbi kudi Naira 5,000 don shiga makaranta ko dan koyan sana'a

Da take jawabi a wajen taron a Kaduna, mataimakiyar gwamnan jihar, Dakta Hadiza Sabuwa, wacce ta wakilici gwamna Nasir El-Rufai, ta ce ilimi da jin dadin yara abu ne mai matukar kima ga gwamnatin su ta bawa a kokarinta na bunkasa rayuwar dan Adam.

Kara karanta wannan

An Gurfanar Da Abubakar A Kotu Kan Satar Burodi A Kaduna

Almajirai
Hoto: Thisday
Almajirai 2,764 Ne Za Su Amfana da Rabon Kudi A Jihar Kaduna
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarta,

Ta ce mun yanke shawarar mayar da ilimi kyauta kuma wajibi ne a farkon shekaru 12 na haihuwa ko kuma na fara yin Makaranta."

Ta bayyana cewa gwamnati ta kuma dauki matakin magance gurbatattun tsarin Almajirci/Tsangaya don ganin ba a bar kowanne wani yaro a baya wajen cin gajiyar ’yancin ilimi ba kamar yadda jaridar Thisday ta rawaito

James Kanyip wanda ya wakilici Sabuwaa, ya ce

Gwamnati na maye gurbin tsarin Almajiri da ake yi a halin yanzu wanda akai tsari da tare dea yin hanyoyi dan kula da al'amuran almajiran
“Don haka ne Malam Nasir El-Rufai ya tabbatar da cewa jihar Kaduna ta kafa dokar kula da yara da kare hakkin yara a shekarar 2018 domin tabbatar da dokar kare hakkin yara tare da kara karfafa manufofi da matakan da ake dauka na inganta samar da ilimi da kiwon lafiya ga dukkan yara. ,”

Kara karanta wannan

2013: Rashin Ganin Shugaban PDP a Wurin Kamfen Atiku a Maiduguri Ya Tada Kura, An Gano Dalili

UNICEF Ta Bawa Jihar Kaduna Tallafi

A cikin wani sakon fatan alheri, kwararre kan kare hakkin yara na UNICEF, Dokta Wilfred Mamah, ya ce UNICEF, tare da hadin gwiwar ma’aikatar kula da ayyukan jin kai ta jihar, sun sami nasarar sake hade yaran Almajirai 10,817 a fadin kasar sakamakon barkewar annobar COVID-19. .

Ya kuma ce an samu kananan yara 209,950 da ke cikin halin da ake ciki a kan titi, ciki har da yara mata matasa a tsarin kula da bayanan kare hakkin yara

A cewar Mamah, akwai Almajirai 105,726 da ba'a kula da su, yayin da akwai mata 104,224 wanda suke yara ba sa zuwa makaranta.

Ya ce

UNICEF ta samu damar yin wadannan ayyuka ga yara 2,674 da suka rage a gidajensu :

Ya yi kira ga gwamnan da ya yi la’akari da gaggauta sakin tallafin da ya dace wanda mai martaba ya yi alkawari a yayin kaddamar da wannan aiki duba da yadda matsalar ta ke.

Asali: Legit.ng

Online view pixel