Cikakken Jerin Yan Kwallon Da Ba Zasu Samu Damar Taka Leda a World Cup Ba Saboda Injury
Yayinda ake saura kwanaki goma (10) kacal da fara gasar kwallon duniya a kasar Qatar, wasu shararrun yan kwallo ba zasu samu damar taka ledar ba saboda raunuka da suka samu.
Gasar kwallon duniyar bana na cike da tarihi da dama.
Wannan shine karon farko da za'a buga gasar a kasar Larabawa sannan kuma karon farko da za'a buga a karshen shekara kuma tsakiyar kakar kwallon kungiyoyin kwallo.
Sakamakon haka, yan kwallo da dama sun samu raunuka yayinda suke takawa kungiyoyinsu kwallo.
A baya da ake buga gasar a tsakiyar shekara tsakanin Yuni da Yuli, yan kwallo na da hutun makonni don murmurewa daga ciwukan da suka samu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ga jerin yan kwallon da ba zaku gani a Qatar ba
Yan Kwallo | Kasarsu |
Sadio Mane | Senegal |
Paul Dybala | Argentina |
Romelu Lukaku | Belgium |
Mike Maignan | Faransa |
Paul Pogba | Faransa |
N’Golo Kante | Faransa |
Timo Werner | Jamus |
Diogo Jota | Portugal |
Georginio Wijnaldum | Netherlands |
Diego Carlos | Brazil |
Arthur Melo | Brazil |
Ben Chilwell | Injila |
Reece James | Injila |
Jesus ‘Tecatito’ Corona | Mexico |
Florian Wirtz () | Jamus |
Kamaldeen Sulemana | Ghana |
Sardar Azmoun | Iran |
Raul Jimenez | Mexico |
Dusan Vlahovic | Serbia |
Son Heung-min | Koriya Ta Kudu |
Yann Sommer | Switzerland |
Ronald Araujo | Uruguay |
Joe Allen | Wales |
Giovani Lo Celso | Argentina |
Raphael Varane | Faransa |
2022 World Cup: Zina haramun ne, Gwamnatin Qatar gargadi masu zuwa
Gwamnatin kasar Qatar ta gargadi duk ami niyyar halartan gasar kwallon duniya da zai gudana a kasar Qatar bana cewa wanda aka kama kebance da wata budurwa ba matarsa zai kwashe shekaru bakwai a magarkama
Gwamnati ta kara da cewa haramun ne shan giya a bainar jama'a a Qatar.
Qatar ta bayyana cewa ko kwayar zarra ba zata canza dokokinta na addinin Islama ba don wani gasar kwallo na kwanaki 21 kacal.
A cewar DailyStar:
"Idan ba miji da mata masu aure ba, basu yarda mutum yayi jima'i ba. Hakazalika babu casu gaba daya. Kowa ya fahimci haka ko kuma a jefashi kurkuku."
"Yan kallo su shirya, babu jima'i da zinace-zinace wannan karon."
Zina, Luwadi da Madigo haramun ne a kasar Qatar, duk wanda aka kama zai iya sha daurin shekaru 7 a gida yari.
Asali: Legit.ng