'Yan Najeriya Ba Zasu Fuskancin Rashin Abinci Ba a 2023, Gwamnatin Buhari

'Yan Najeriya Ba Zasu Fuskancin Rashin Abinci Ba a 2023, Gwamnatin Buhari

  • Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta bayyana tanade-tanaden da take yi don tabbatar da tsaron abinci a fadin kasar nan
  • Ministan noma, Mohammad Abubakar, ya yi watsi da rade-radin da ke yawo cewa za a yi fama da karancin abinci a Najeriya a 2023
  • Abubakar ya ce gwamnati ta tanadi wasu manufofi da suka hada da bayar da tallafin taki ga manoma, inganta noma da sauransu don rage tsadar rayuwa

Abuja - Gwamnatin tarayya ta sake yin watsi da ikirarin cewa kasar za ta fuskanci karancin abinci a cikin shekara ta 2023, Channels TV ta rahoto.

Ministan noma, Mohammad Abubakar, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 9 ga watan Nuwamba, bayan taron majalisar zartarwa.

Buhari
'Yan Najeriya Ba Zasu Fuskancin Rashin Abinci Ba a 2023, Gwamnatin Buhari Hoto: Nigerian Tribune
Asali: UGC

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, me ya jagoranci zaman majalisar na yau Laraba a fadar shugaban kasa, jaridar Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sauye-Sauyen NNPC: "Rayuwa Ta Na Cikin Hatsari", Kyari Ya Yi Magana Kan Barazanar Kashe Shi

Abubakar ya bayyana cewa gwamnati na aiki don rage tsadar rayuwa da kuma tabbatar da tsaron abinci ta hanyar bayar da tallafin taki, inganta noma da kuma hana fataucin kayan abincin da sauran dabaru.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin watanni biyu da suka gabata, gidaje da gonaki sun nutse a ruwa a jihohin Lagas, Yobe, Borno, Taraba, Adamawa, Edo, Delta, Kogi, Niger, Plateau, Benue, Ebonyi, Anambra, Bauchi, Gombe, Kano, Jigawa, Zamfara, Kebbi, Sokoto, Imo, Abia da babban birnin tarayya.

A cewar hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA), kimanin mutane 600 ne suka mutu yayin da wasu miliyoyi suka rasa muhallansu saboda mummunar ambaliyar ruwa da ta afkawa jihohi fiye da 20 cikin yan watannin da suka gabata.

Ambaliyar ruwa da aka yi fama da ita a 2022 ta ja hankalin kasashen duniya. A wata wasika da ya aikewa shugaban kasa Muhammadu Buhari, King Charles II ya tausayawa Najeriya kan wannan annobar da ta afka mata.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Kotu ta daure mai gadi a jihar Arewa bisa laifin barci a bakin aiki

Jawabin wasu manoma

Legit.ng ta zanta da wani manomi mai suna Mallam Yusuf don jin ta bakinsa game da wannan hasashe inda ya nuna lallai akwai aiki ja a gaban gwamnati don dakile wannan lamari.

Mallam Yusuf ya ce:

"A ɗan karamin tunani na da hange na dole sai gwamnati ta tashi tsaye sannan zata iya daƙile karancin abinci a shekara mai zuwa.
"Duk da munsan tashin farashi ko muce tsadar rayuwa Global issue ne amma idan ana maganar abinci mu da muke karkara mu muka san zahirin yadda abun yake.
"Kinga damunar bana ta zo jarabawa iri daban-daban, na farko tsadar kayayyi wani manomin ko ya siyar da kayan nomansa na bara kudin ba zasu isa ya sake yin wani noman bana ba.
"Ambaliya ta zo ta ci iya nata, yawan ruwan da aka yi bana ya lalata amfanin gona.
"Sannan wata jarabawa bana ga zaki ga noma ya yi kyau gwanin sha'awa a gona amma Allah ya kwashe albarkar da an yi girbi inda mutum ya saba samun buhu 100 wlh bana da wuya ya sami 30.

Kara karanta wannan

An shiga jimami yayin da gobara ta yi kaca-kaca da makarantar Tsangya a Kano

"Ni manomi ne kuma tabbaas bana an samu jarabawa fiye da tsammani amma muna yi wa gwamnatin Buhari kyakkyawan zato su samu ikon shawo kan lamarin nan domin Talaka a yanzun dole ya siyar da amfanin gona kuma nan gaba dole zai nema idan babu ya zaai.
"Tabbas akwai barazana muna dai fatan Allah ya fitar da mu."

A nashi bangaren, wani manomi mai suna Mallam Ibrahim ya ce:

"Ba karancin muke tsoro ba, wasu mutane suna ta siyan kayan abinci suna boyewa. Kamar ni yanzu, na yi noma, wasu har gona suka zo neman na siyar musu da amfanin gona ta, amma na ki saboda bansan me zai biyo baya ba, kuma sun saka kudi da yawa.
"Hakan ya bani tsoro, domin a gaba tabbas abinci zai yi karancin da ake tsoro. Fatan mu gwamnati ta yi wani abu don mu samu mu tsira, yanzu haka albashin N100,000 ba ya isar mu iya ciyar da ahalinmu."

Kara karanta wannan

Allah ya yiwa wani babban jigon tawagar kamfen Atiku a Abuja rasuwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel