Fitaccen Dan Kwallon Kafa, Didier Drogba Ya Karyata Shiga Addinin Muslunci

Fitaccen Dan Kwallon Kafa, Didier Drogba Ya Karyata Shiga Addinin Muslunci

  • Fitaccen tsohon dan kwallon kafan Chelsea ya bayyana gaskiyar magana kan labarin da ke yawo na sauya addininsa
  • An yada hotuna da ke nuna lokacin da Drogba ke addu'a yana zaune kamar dai yadda Musulmai ke yi
  • A rubutun da ya yi, ya warware zare da abawa, ya bayyana gaskiyar abin da ya faru da kuma matsayarsa kan addini

Fitaccen dan kwallon kafa na kasar Ivory Cost, Didier Drogba ya karyata labarin da ake yadawa na cewa ya karbi addinin Muslunci.

Wasu rahotanni a baya kadan sun ruwaito tare da yada hotunan lokacin da aka ce Drogba ya ayyana shahadar shiga Muslunci.

An ga hotunan lokacin da Drogba ke dage da hannu yana addu'a kamar dai yadda Musulmai ke yi.

Alamu sun nuna wannan ne yasa kafafen yada labari manya suka dauki labarin cewa ya sauya addini.

Kara karanta wannan

Bacin rana: Kotu ta daure mai gadi a jihar Arewa bisa laifin barci a bakin aiki

Drogba ya magantu kan rade-radin shigarsa Muslunci
Fitaccen Dan Kwallon Kafa, Didier Drogba Ya Karyata Shiga Addinin Muslunci | Hoto: ghanaweb.com
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai, a jiya Litinin 7 ga watan Nuwamba, dan wasan ya yada wani batu mai daukar hankali a shafinsa na Twitter, inda ya ayyana gaskiyar abin da ya faru.

'Yan uwa na na ziyarta, ban karbi Muslunci ba, inji Drogba

A rubutun da ya yi, ya shaidawa duniya cewa, ya kai ziyara ne kauyensu, inda ya gana da wasu 'yan uwansa Musulmai.

Ya kuma bayyana cewa, yana nan kan addinin da yake atun farko, bai sauya addini ba, kawai jita-jita ake yadawa.

Ya rubuta cewa:

"Wannan labari na ta karade intanet amma ban sauya addini ba.
"Kawai dai ni ne a lokacin da nake mutunci da 'yan uwana Musulmai da na ziyarta a kauye. Lokacin kusantaka."

Fitattun Jagororin Jam'iyyar PDP Sun Koma APC A Jihohin Sokoto da Zamfara

A wani labarin, Alhaji Sahabi Bojo-Bodinga, fitaccen jigon jam'iyyar PDP a jihar Sokoto ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC tare da dimbin magoya bayansa.

Kara karanta wannan

Za mu zama marasa amfani idan muka bari Tinubu yaci zabe, Kiristocin Arewa

Sahabi ya samu tarba ne zuwa APC daga babban mai tafiyar da ita a jihar Sokoto, Sanata Aliyu Wammako a gidansa da ke Sokoto a ranar Juma'a 4 ga watan Nuwamba, The Nation ta ruwaito.

Hadimin Wammako a harkokin yada labarai, Bashar Abubakar ya bayyana shigowar Sahabi APC a matsayin nasara da karin ci gaba ga jam'iyyar a zaben 2023 mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.