Babu Maganar Cire Rubutun Ajami, Kirkirar N2,000, 5,000, 10,000a Takardar Naira, Inji CBN
- Babban bankin Najeriya ya bayyana matsayarsa kan halin da ake ciki na yadda yake sauya fasalin kudin kasar
- Ana ta yada jita-jitan cewa, gwamnatin Najeriya na shirin kirkirar manyan kudaden da suka kai N2,000, N5,000 da N10,000
- Hakazalika, wasu na yada jita-jitan cewa, ana shirin cire rubutun Ajami da ya dade a kudin kasar, CBN ya yi bayani
FCT, Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya magantu kan cece-kuce da jita-jitan da ake yadawa kan kirkirar sabbin kudi a Najeriya, ciki har da N2,000, N5,000 da N10,000.
Rahotanni sun bayyana a kafafen yada labarai na Najeriya kan sauya fasalin kudi a kasar, inda babban bankin da shugaban kasa Buhari suka tabbatar da hakan.
Tun bayan fitowar maganar sauya fasalin kudi, batutuwa suka fara fitowa kan yadda sauyin zai kasance; wasu sun ce za a cire Ajami, wasu kuwa suka ce za a kirkiri gudan N2,000, N5,000 har ma da N10,000.
Babu batun kawo sabon N2,000, N5,000 da N10,000
Sai dai, daraktan kudi na CBN, Ahmed Bello Umar ya yi karin haske, ya rushe batutuwan da ke yawo, inda yace sam babu wannan batu na kirkirar sabon kudi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan rediyon Muryar Amurka a ranar Litinin 7 ga watan Nuwamba, inda yace babban kudi a Najeriya har yanzu N1,000 ne.
A cewarsa:
"Gaskiya shi ne, ba wani karin sabon kudi da za a yi sama da N1,000. Saboda haka ba N2,000, ba N5,000 ko wani N10,000 da suke magana a kai.Kudi mafi daraja a ciki N1,000 ne."
Daga nan ya bayyana cewa, bayan kaddamar da kudaden da aka sauya fasalinsu kamar yadda shugaban kasa ya bayyana.
Babu batun cire Ajami a kudin Najeriya
Yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan batun Ajami da ke jikin kudi, ya yi tsokaci kan matsayar babban bankin Najeriya.
Idan baku manta ba, ya zuwa yanzu akwai batutuwa a gaban kotu da ke neman a cire Ajami a jikin kudin kasar.
Wasu kuwa a kasar, sun nuna sam ba zai yiwu a cire wannan rubutu ba.
A nasa jawabin, daraktan kudi ya ce ba abin damuwa bane, don haka 'yan Najeriya su kwantar da hankali, ba za a cire Ajami ba, kamar yadda ya shaidawa VOA.
Ya kuma shawarci mutane su kula, kana su sanar da hukumomin tsaro kan duk wani mai shirin nuna musu an kirkiri gudan N2,000, N5,000ko N10,000.
Naira da Cedi Na Fafatawa a Matsayin Kudi Mafi Muni a Nahiyar Afirka a 2022
A wani labarin, Steve Hanke, farfesan tattalin arziki kuma daraktan Troubled Currencies Project a kasar Amurka ya buga wani rahoton mako mai nuna kudaden da suka gamu da raguwar daraja da akalla 20% na dalar Amurka.
Hanke ya bayyana cewa, kudaden da ya tattaro a jerinsa sun gamu da raguwar daraja ne cikin shekaru biyu kacal.
Business Insider ta ruwaito cewa, wannan jeri na Hanke ya nuna adadin hauhawar farashin kayayyaki da kuma raguwar darajar kudi a kasashen.
Asali: Legit.ng