Sauya Fasalin Naira: Gwamnan CBN Ya Umurci Dukkan Bankuna Su Fara Budewa Ranar Asabar

Sauya Fasalin Naira: Gwamnan CBN Ya Umurci Dukkan Bankuna Su Fara Budewa Ranar Asabar

  • Bankin CBN ya yi kira ga yan Najeriya su gaggauta kai kudadensu banki ko da ranar Asabar ne
  • Dirakta Sadarwan CBN ya ce an umurci dukkan bankuna su fara bude ofishohinsu ranar Asabar
  • A ranar 16 ga Oktoba, bankin CBN ya sanar da sauya fasalin Naira, Shugaba Buhari yace hakan daidai ne

Kwara - Babban Bankin Najeriya CBN, ya umurci dukkan bankunan dake Najeriya su fara budewa kofofinsu ranar Asabar daga yanzu zuwa ranar 31 ga Junairu don mutane su samu damar mayar da kudadensu.

Legit ta kawo muku rahoton cewa ranar 15 ga Disamba, 2022, bankin CBN zai fitar da sabbin takardun Nairan N200, N500, da N1,000.

Diraktan Yada Labaran Bankin, Osita Nwasinobi, ne ya sanar da wannan umurni da aka yiwa bankunan.

Ya bayyana hakan ne a wani taron baja kolin CBN da ya gudana ranar Alhamis a Ilori, birnin jihar Kwara, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Karban Bashin Fa Ya Isa Haka, Ofishin Tattalin Basussuka DMO Ya Gargadi Gwamnatin Buhari

Emefiel
Sauya Fasalin Naira: Gwamnan CBN Ya Umurci Dukkan Bankuna Su Fara Budewa Ranar Asabar Hoto: Emefiele
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nwasinobi ya samu wakilcin mukaddashin Diraktan sadarwan bankin, Akpama Uket.

Jawabin da Yayi:

"An umurcesu su fara karban kudaden Naira koda nawa ne duk da hakan ya sabawa tsarin da aka shirya."
"Saboda haka ya zama wajibi ku mayar da dukkan kudaden N200, N500 da N1000 banki kafin karewar wa'adin."

Ku Kawo Kudadenku kan su zama banza: Jerin Bankunan Da Suka Kara Ranakun Aiki kwo yanzu

Biyayya ga umurnin CBN na tattara kudaden Naira dake yawo cikin jama'a, wasu bankuna sun sauya lokutan aikinsu don mutane su samu damar kai kudadensu.

A sakon akwatin email da suka aikawa kwastamominsu, bankunan sun bayyana cewa sun sauya ranakun aikinsu ne don taimkawa kwastomomi wajen zuba kudadensu a banki kan ranar 31 ga Junairu da CBN ya bada wa'adi.

Bankunan da aka ga sanarwarsu kawo yanzu sun hada da Ecobank, UBA da Access Bank.

Kara karanta wannan

Sauya Fasalin Naira: Miyetti Allah Ta Roki CBN Ya Kara Wa'adi Saboda Kada Fulani Suyi Hasara

Sauya Fasalin Naira: Miyetti Allah Ta Roki CBN Ya Kara Wa'adi Saboda Kada Fulani Suyi Hasara

Kungiyar Fulani Makiyaya Miyetti Allah (MACBAN) ta bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) ya tsawaita ranar kai tsaffin kudi banki da akalla watanni uku.

Shugaban kungiyar na yankin kudu maso gabas, Alhaji Gidado Siddiki, ya bayyana hakan ne a hirar da ya gabatar da Awka, babbar birnin jihar Anambra ranar Alhamis, 17 ga Nuwamba, 2022, rahoton Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel