Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Naira Biliyan 2 Wajen Siyo Sabbin Motoci
- Yayinda ake kukan bakudi, ba kudi, gwamnatin tarayya na shirin sayan sabbin motocin fadar Aso Villa
- An ware kimanin naira bilyan biyu a kasafin kudin 2023 don yiwo wannan sayayya mai tsada
- Shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudi gaban majalisar dokokin tarayya a watan Oktoba
Abuja - Baban sakataren fadar shugaban ƙasa, Tijjani Umar, ya bayyana buƙatar sauya wa gidan gwamnati motocin hawansu kamar yadda Premium Times ta rawaito.
A yayin da yake bayyana dalilin hakan, sakataren ya nuna irin buƙatar da take akwai na zirga-zirga a-kai-a-kai saboda zaɓukan da za a gabatar.
Wannan ce ta sa akwai buƙatar dogo su waɗancan fyalla-fyallan motoci, inda shugaba Buharin zai kashe har Naira biliyan 1.96.
Wannan na zuwa ne baya ga irin matsalar tattalin arziƙi da ƙasar ke fama da shi da kuma faɗuwar darajar Naira da ma basussuka na 'yan kwangila da ke wuyan gwamnatin na tiriliyoyin nairori.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yayin kare kasafin kuɗin shekara mai zuwa na Fadar Shugaban Ƙasa a gaban wani kwamiti na majalisar dokoki, sakataren ya tabbatar da cewa lokaci ya yi da ya kamata a canja motocin.
Yana mai cewa musamman idan aka yi la'akari da dokar hukumar zaɓe da ta haramta amfani da kayan gwamnati ga kowacce jam'iyyar siyasa.
"Rashin canja sun na haifar da lalacewar motocin a-kai-a-kai da kashe kuɗi ba-gaira-ba dalili wajen gyara ko canja musu wasu sassa," In ji Sakataren.
Haka kuma sakataren ya bayyana cewa mafi yawan motocin da za a siyo da waɗannan maƙudan kuɗaɗe, za ayi amfani da su ne wajen tafiye-tafiye a wanann lokaci da zaɓukan ƙasar ke ƙaratowa.
Sai dai ya koka kan yadda ba lallai ne waccan biliyan ɗaya "ta isa wajen samar da abin da ake da buƙata ba saboda halin tsantseni na gwamnati"
Sannan sakataren ya tabbatar da cewa kasafin kuɗin fadar gwamnati na shekarar 2023 wanda zai kama biliyan ashirin da ɗaya da ɗoriya bai kai na shekarar 2022 idan aka kwatanta su.
A kasafin fadar shugaba Buhari na wannan shekara mai ƙarewa an fitar da Naira biliyan arba'in ne wanda idan aka kwatanta da na shekara mai zuwa, ya ragu da kashi 19 cikin 100.
Kenan, a cewarsa, za a kashe kusan kaso sittin da biyar wajen siyo kayayyaki a fadar gwamnati da jumullar kuɗi Naira biliyan bakwai da ɗoriyi, riwayar Guardian.
Abubuwa sun yi tsada
Kuma tun a farkon wannan shekara ne, wata Ƙungiyar Tuntuɓa ta Ma'aikata (NECA) ta ja hankalin shugaban ƙasa game da tsadar kayayyaki da na makamashi da na faɗuwar darajar Naira wadda ke cigaba da ruguza tattalin arziƙin Najeriya.
Babban Darakta na wannan ƙungiya, Wale Oyerinde, ya kuma ce rashin kyakkyawan tsari na hukumar Jiragen Sama da Tsarin Ilimi da ƙaruwar basussuka da rashin wadataccen kuɗin ajiya a asusun Najeriya na ƙasar waje da tsadar man fetur; su ne dalilan da ke ƙara sa tattalin arziƙin gurguncewa.
Ko da a watan Agusta, Ministan Ƙwadago, Chris Ngige, ya tabbatar da cewa gwamnatin Nijeriya ba ta da kuɗin da za ta iya gabatar da manyan ayyuka a shekara mai zuwa.
"Kamar yadda kuke gani, farashin dala ɗaya Naira 500 ne zuwa 600, amma a yanzu ta kai Naira 700.
A gaskiya, ba kuɗi kwata-kwata. Kuɗin da Kwamitin Ajiyar Kuɗi na Gwamnatin Tarayya (FAAC) ke rabawa na samuwa ne daga kuɗaɗen haraji da kuma sauran sassan hukumomi masu samar da kuɗin shiga na ƙasa."
Asali: Legit.ng