An Ci Karo da Matsaloli, Gwamnatin Buhari Za ta Iya Shirya Sabon Kundin Kasafin kudi
- Idan aka tafi a haka, ba abin mamaki ba ne gwamnatin tarayya ta gabatar da sabon kundin kasafin kudi
- A halin yanzu Naira tana cigaba da karyewa a kan Dalar Amurka, kuma kaya su na kara tsada a kasuwa
- Wasu masana sun tafi a kan cewa sai an yi kwaskwarima, gwamnati tayi amfani ne da tsarin MTEF/FSP
Abuja - Babu mamaki gwamnatin tarayya ta gabatar da wani sabon kasafin kudi ga majalisar tarayya saboda halin tattalin arzikin da kasa ta shiga.
Punch ta rahoto cewa yadda darajar Naira take faduwa a kasuwa da hauhawar farashin kaya sun jawo nakasa ga kundin kasafin kudin 2023.
A kasafin kudin shekara mai zuwa, Gwamnatin Muhammadu Buhari tayi lissafin farashin Dala a kan N435 da tashin farashin kaya a kan 17.10%.
Amma a halin yanzu Naira tana karyewa, farashin Dala a babban bankin CBN zai iya kai N500, ana hasashen a kasuwar canji, Dala za ta iya kai N1000.
Yakin Rasha da Ambaliyar ruwa
Tun yanzu ta kai ‘yan canji a Legas da Abuja su na saida $1 kan N895. Yakin Rasha da Ukraine kuma zai jawo kaya su cigaba da kara tsada a Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Baya ga yakin da ya ki ci, ya ki cinyewa, za a gamu da tasirin ambaliyar ruwan sama a kakar bana. Wannan matsalar za ta shafi manoma a jihohi.
Street Journal tace ‘yan majalisar tarayya sun shirya amincewa da kasafin kudin a yadda aka gabatar masu da shi, duk da bambancin da ake samu.
A ranar Alhamis aka fahimci akwai yiwuwar majalisa ta bukaci gwamnati ta turo da sabon kundin kasafin kudi da zai yi la’akari da halin tattalin kasar.
Tsarin MTEF/FSP zai yi aiki?
Wata majiya a majalisar wakilai tace da wahala su taba lissafin kasafin kudin kasar na 2023 domin an yi la’akari ne da tsarin tattalin arzikin MTEF/FSP.
A hasashen MTEF/FSP, shugaba Muhammadu Buhari ya yi lissafin farashin gangar danyen mai a $73, amma a kasafin shekarar badi, ya yi amfani da $70.
Da aka tambayi mataimakin shugaban kwamitin kasafi, Hon. Iduma Igariwey kan batun, yace zai bukaci lokaci ya tuntubi shugabansa, Hon. Aliyu Betara.
"Akwai gyara a kasafin 2023"
Amma masana irinsu shugaban kuniyar NACCIMA, John Udeagbala sun ce akwai matsala tattare da kundin kasafin kudi, musamman a lissafin Dala.
Farfesa Sheriffdeen Tella mai koyar da ilmin tattali da tsimi a jami’ar Olabisi Onabanjo yace Dala za ta kai N1000, hakan yana nufin sai an ci bashi.
Aikin kwamitin kudi a Majalisa
An samu rahoto Majalisar Wakilan Tarayya ta bada kwanaki bakwai domin ganin Ministar tattalin arziki da kuma Akanta Janar na kasa a gaban ta.
Baya ga haka, kwamitin da Hon. Oluwole Oke yake jagoranta yana neman zama da Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Folashade Yemi-Esan.
Asali: Legit.ng