Rabin Albashi: Kwanaki 20 da Janye Yajin-Aiki, ASUU Za Ta Kira Taron Gaggawa
- Alamu na nuna Malaman jami’a da ke karkashin kungiyar ASUU za suyi zaman majalisar NEC
- Kungiyar ASUU za tayi taro a dalilin biyan malaman jami’a rabin albashi da aka yi a watan Oktoba
- Gwamnati ba ta biya ‘yan kungiyar ASUU da CONUA duka kudinsu ba duk da an daina yajin-aiki
Abuja - Ana sa ran kungiyar malaman jami’a na kasa watau ASUU, za ta kira taron gaggawa na majalisar koli a game da batun albashin ‘ya ‘yanta.
Punch ta fitar da rahoto a ranar Juma’a, 4 ga watan Nuwamba 2022, wanda ya nuna cewa akwai yiwuwar ASUU tayi zaman NEC ba da dadewa ba.
Zuwa yanzu ba a sa rana ba, amma alamu na nuna malaman jami’an za suyi taro na gaggawa kan batun rabin albashin Oktoba da gwamnati ta biya.
Shugaban kungiyar ASUU na kasa, Farfesa Emmanuel Osodeke ya shaidawa jaridar cewa ba a biya su cikakken albashinsu duk da sun koma aiki ba.
ASUU za ta zauna - Emmanuel Osodeke
Emmanuel Osodeke ya nuna cewa shugabannin kungiyar malaman jami’an za suyi zaman gaggawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“An biya rabin albashi, ba a bada wani dalili ba. Mun fahimci Chris Ngige ya rubutawa ofishin Akanta Janar da IPPIS cewa a biya mu na lokacin da muka janye yajin-aiki ne kawai.
“Mun ji labari an rubuta takarda a game da wannan, amma ba mu ga takardar ba. Za mu kira taro.”
Babu ruwan Ma'aikatar ilmi
Da aka tuntubi ma’aikatar ilmi domin jin abin da ya faru, tace ba ta da alhakin biyan albashi.
Kakakin ma’aikatar, ya bayyana cewa aikinsu shi ne kula da jami’o’in Najeriya, a game da abin da ya shafi biyan albashi, a tuntubi Akanta Janar.
Abin ya shafi kowa?
Premium Times tace gutsuren albashi da aka biya ya shafi ‘yan kungiyar ASUU da CONUA, amma ana zargin an biya likitoci cikakken albashinsu.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa malaman da ke jiran a biya su albashinsu na wata da watanni, sai suka ji an biya su rabin da suke karba a duk wata.
Wani malamin jami’ar Uniport a jihar Ribas ya nuna an aiko masa da N80, 000 a akawun.
Wata malama da ke karantarwa a jami’ar tarayya da Dutsinma a Katsina ta fusata da ta ga an biya ta rashin albashinta, tace ta rasa me za tayi da shi.
Yajin-aikin ASUU
Ana da labari a shekarar nan, an yi ta fama da yajin-aiki kungiyar ASUU, sai kwanan nan babban kotun daukaka kara ta umarci a dawo bakin aiki.
Kafin nan an shafe watanni kusan takwas a gida ba tare da an iya ci ma matsaya tsakanin gwamnatin Muhammadu Buhari da kungiyar ASUU ba.
Asali: Legit.ng