Tsohon Shugaban Kamfanin Twitter Dorsey Zai Kaddamar da Sabuwar Manhajar Sadarwa

Tsohon Shugaban Kamfanin Twitter Dorsey Zai Kaddamar da Sabuwar Manhajar Sadarwa

  • Bluesky ce sabuwar manhajar sada zumunta da tsohon mai kamfanin Twitter Jack Dorsey ya kirkira
  • An fara aiwatar da aikin habaka manhajar ne a 2019, kuma za ta zo sabbin tsaruka daban da sauran shafukan sada zumunta
  • Ana ta cece-kuce a duniya tun bayan da Elon Musk ya bayyana karbar ragamar kamfanin Twitter

Yayin da Elon Musk ya kammala karbar ragamar tafiyar da Twitter bayan biyan kudinta, Jack Dorsey, tsohon shugabanta zai kaddamar da sabuwar manhayar sada zumunta.

Idan baku manta ba, Dorsey ya siyarwa Musk kamfanin Twitter, kana ya ba shi ragamarta a wannan shekarar bayan dogon cece-kuce.

An ruwaito cewa, a yanzu Dorsy zai mayar da hankali ne wajen habaka sabuwar manhaja mai suna Bluesky Social, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Jack Dorsey zai kirkiri sabuwar manhajar sada zumunta
Tsohon Shugaban Kamfanin Twitter Dorsey zai kaddamar da sabuwar manhajar sadarwa | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A cewar Dorsey, Bluesky ba za ta zama kishiya ga Twitter ba kamar yadda za a yi tunani, sai dai ma ta zama kishiya ga duk wani kamfanin sada zumunta da ke da shirin kwaikwayar sabon tsarin bai daya da zai ta zo dashi.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya fadi wadanda zai siyarwa matatun man Najeriya idan ya gaji Buhari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kori manyan shugabannin Twitter

Mako guda kafin Musk ya karbi ragamar, ya sallami wasu manyan masu kula da kamfanin uku, ciki har da Parag Agrawal.

Tuni dai Parag Agrawal da Jack Dorsey suka sanar da fara neman masu gwada wannan sabuwar manhaja da suka kirkira, Rahoton Tech Economy.

A hankali, Dorsey na kokarin samar da kafar da za ta zama mafaka ga wadanda ka iya tunzura ga sabbin tsarukan tafiyar da Twitter.

Bluesky dai an assasa ta ne a shekarar 2019 domin saukakawa da samar da manhajar sada zumunta ta musayar bayanai kai tsaye, kuma an yi ta a baya a karkashin Twitter.

Elon Musk: Za Mu Dawo Da Shafukan Mutanen Da Aka Toshe A Twitter

A wani labarin, sabon mammalakin Twitter, Elon Musk a ranar Laraba ya ce nan da makonni kadan za a bude shafukan mutanen da aka dakatar da su - kamar tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Elon Musk: Za Mu Dawo Da Shafukan Mutanen Da Aka Toshe A Twitter

Masu amfani da Twitter suna sa ido su gani ko Musk zai bude shafin Trump da aka dakatar saboda tunzura mutane yin boren ranar 6 ga watan Janairu a ginin majalisar dokoki a Washington.

Dawo da irin wadannan shafukan da aka toshe saboda saba dokokin dandalin zai iya zama manuniya kan inda dandalin zai fuskanta a karkashin shugabancin Musk, wanda ke bayyana kansa a matsayin 'mai son ganin kowa ya samu yancin tofa albarkacin bakinsa'.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.