PDP ga Shettima: Cutar Mantau Ke Damunka, Gidanku Yana Ci da Wuta, Ku Fara Magance shi

PDP ga Shettima: Cutar Mantau Ke Damunka, Gidanku Yana Ci da Wuta, Ku Fara Magance shi

  • Daraktan sadarwa na tawagar kamfen din Atiku Abubakar, Dele Momodu, ya kwatanta Kashim Shettima da mai cutar mantau wanda yake hangen wasu bayan ga matsala cikin gidansu
  • Momodu yace matsalolin da suka yi wa APC yawa ne yasa suka dauka dogon lokaci basu fitar da tasatar kamfen din shugabancin kasa ba sai daga baya
  • Shettima dai a ranar Talata yace zasu yi wa Atiku ritayar siyasa a 2023 ya koma Dubai, kuma yafi dacewa da duba-gari fiye da shugabancin kasa

Legas - Babbar jam’iyyar hamayya ta Najeriya, PDP a ranar Laraba tayi martani kan ‘dan takarar mataimakin shugabancin kasa na APC, Kashim Shettima, da ya kwatanta ‘dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar da ‘dan siyasa mai yawon bude ido wanda zai yi murabus din dindindin a Dubai bayan zaben 2023.

Kara karanta wannan

Atiku Fa Aikinsa Sayar Da Ruwan Gora, Za Muyi Masa Ritaya Ya Koma Dubai: Kashim Shettima

Atiku da Shettima
PDP ga Shettima: Cutar Mantau Ke Damunka, Gidanku Yana Ci da Wuta, Ku Fara Magance shi. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Shettima ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da alkawurran APC ga ‘yan kasuwa da bangarori masu zaman kansu a Legas ranar Talata.

Ya duba Atiku tare da tuhumar takardun karatunsa. Yace satifiket din Atiku na makarantar tsafta ta jihar Kano ya zama matakin cancantarsa na zama duba gari.

Premium Times ta rahoto cewa, Shettima ya kara da zunden Atiku kan dogon tarihin da yake da shi na neman kujerar shugabancin kasa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Martanin PDP

Amma jam’iyyar PDP a ranar Laraba ta hannun daraktan sadarwa na tawagar kamfen din shugabancin kasa, Dele Momodu, yace Shettima yana fama da cutar mantau kuma babu ‘dan takarar APC da zai iya hada kan Najeriya bayan sun nuna kyamarsu ga damokaradiyya da hakkin kada kuri’a ga wasu kabilu cikin kasar.

Kara karanta wannan

Sarakuna 17 Sun Yi Watsi da Atiku, Sun Karyata Batun Goyon Bayan Takararsa

“Cike da mamaki muka kalla bayanan da ‘dan takarar mataimakin shugaban kasan APC, Alhaji Kashim Shettima yayi a wani taro a Legas. Ya zargi cewa Atiku ba zai iya hada Najeriya ba tunda bai hada kan jam’iyyarsa ba.
“Mun yarda cewa cikin halin cutar mantau da Shettima ke ciki yayi kokarin zunden wani bayan ga abubuwan zunde nan tare da shi.
“APC cike da rikici da manyan mambobinta kai tsaye ta bai wa ‘yan Najeriya hakuri kan azabar da ta janyo musu tun 2015. Wannan yana daga cikin dalilan da suka sa mambobin APC suka dinga komawa PDP.
“Sai da aka kwashe lokaci mai tsawo kafin APC ta fitar da tawagar kamfen din shugaban kasanta saboda rashin hadin kan jam’iyyar. Abun takaici ne yadda APC ta tabarbare kuma da yawa daga cikin mambobinta ke tsalle tare da murmurewa a PDP.”

- Momodu yace.

PDP a dabaibaye take da kitimurmura, ba ta da mafita nan da zabe mai zuwa, inji APC

Kara karanta wannan

Sifeta Janar Ya Bayyana Dalilin Da Ya Hana Su Kamawa da Gurfanar da Tinubu

A wani labari na daban, Felix Morka, kakakin jam'iyyar APC ya bayyana irin halin matsi da rikici da jam'iyyar adawa ta PDP ke ciki a halin yanzu, The Cable ta ruwaito.

Ya bayyana hasashensa game da makomar PDP a yayin tattaunawa da gidan talabijin na Legas a ranar Laraba, inda yace ba zai yiwu PDP ta warware damuwar da take ciki ba nan da zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng