Yadda ‘Dan Sanda Ya Nadawa ‘Yar Sanda Matar Aure Duka Don Ta Ki Karbar Soyayyarsa

Yadda ‘Dan Sanda Ya Nadawa ‘Yar Sanda Matar Aure Duka Don Ta Ki Karbar Soyayyarsa

  • IGP Baba Usman Alkali ya bukaci tsatsauran bincike kan bidiyon dake yawo na wata ‘yar sanda da abokin aikinta ya lakada mata mugun duka
  • A bidiyon, ‘yar sanda Bamidele ta zargi Matthew da yi mata duka tare da bata sunanta bayan ta ki karbar soyayyarsa saboda tana da aure
  • Bamidele tace Matthew ya yaga mata suttura inda yayi mata duka tare da ji mata rauni a kirji, kafafu da sauran sassan jikinta a jihar Osun

Osun - Sifeta janar na ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya umarci kwamishinan ‘yan sandan jihar Osun, Olaleye Faleye da ya bincike zargin cin zarafin wata sifetan ‘yar sanda mai suna Bamidele Olorunsogo da DCO din ta Ajayi Matthew yayi a Ode-Omu ta jihar.

Bamidele
Yadda ‘Dan Sanda Ya Nadawa ‘Yar Sanda Matar Aure Duka Don Ta Ki Karbar Soyayyarsa. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Wannan na zuwa ne bayan bidiyon dake nuna shaidar mugun dukan da aka yi wa Bamidele ya yadu a kafafen sada zumuntar zamani.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Gurfana a Kotu Kan Zargin Mazge Matar Aure Har Cikinta Ya Zube

Bidiyon Bamidele ya yadu

A bidiyon, Bamidele ta zargi abokin aikinta a ofishin ‘ya sanda na Omu a jihar Osun da cin zarafinta tare da bata mata suna.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jaridar Punch ta rahoto cewa, ‘yar sandan ta zargi cewa Matthew ya bukaci ta zama budurwarsa amma ta ki amincewa saboda tana da aure, sai dai Matthew ya cigaba da bata mata suna inda daga bisani ya lakada mata duka.

Tace:

“Mene ne laifina? Ya fara dukana har ta kai ga ya cire min kaya. Ku kalla kirjina, kafaduna da ko ina, duk raunika ne. Sunansa Ajayi Matthew. Ya bukaci mu kulla alaka amma nace a’a saboda ina da aure.
“Daga nan ya fara bata min suna inda yake ikirarin cewa dama shi saurayina ne, wanda ba hakan bane.”

Duk kokarin da aka yi na jin ta bakin Matthew kan wannan zargin ya gagara saboda ya ki daukan kiran da aka dinga masa.

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

Sai dai, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi, yayin da aka tuntubesa yace hedkwatar na jiran rahoton bincike daga rundunar ta jihar Osun kafin a dauka matakin da ya dace.

“Zamu jiraci rahoto kan binciken daga rundunar ‘yan sandan jihar Osun kafin daukar matakin da ya dace.
“Sai dai muna tabbatarwa da jama’a cewa za a yi adalci a kan wannan lamarin tare da kiyaye dukkan dokokin aikin ‘yan sandan Najeriya.”

- Adejobi yace.

An Kama Mata Da Miji Saboda Lakadawa Dan Sanda 'Duka' a Legas

A wani labari na daban, an kama wasu mata da miji saboda kai wa dan sanda hari a Oluwaga, Iparaja a Legas.

Wani bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta, ya nuna lokacin da matar ke kaiwa dan sandan hari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel