Wata Mata Ta Kai Karar Tsohon Mijinta Gaban Kotun Musulunci Kan Cikin Da Take Dauke Da Shi

Wata Mata Ta Kai Karar Tsohon Mijinta Gaban Kotun Musulunci Kan Cikin Da Take Dauke Da Shi

  • Wata mata, Ummulkhairi Salisu, ta kai ƙarar tsohon mijinta gaban Kotu kan cikinsa da take ɗauke da shi
  • Matar ta hannun lauyanta ta roki Kotu ta umarci wanda take ƙara ya rinka biyanta N30,000 duk wata na kula da cikin
  • Wanda ake ƙara ya gaya wa Kotun cewa yana sane da juna biyun da take ɗauke da shi amma karfinsa zai iya biyan N2,000 ne kacal

Kaduna.- Wata mata mai ɗauke da juna biyu, Ummulkhairi Salisu, ranar Talata ta roki Kotun Shari'a dake Magajin Gari, Kaduna ta umarci tsohon mijinta, Hassan Malam ya rika biyanta alawus ɗin kula da ciki N30,000 duk wata.

Ummulkhairi, ta bakin lauyanta, Malam N.T. Abdullahi, ta bukaci Kotun ta tabbatar da saki ɗayan da tsohon mijin ya ambata mata, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Wani Mummunan Ibtila'i Ya Halaka Mata da Miji Da 'Ya'yansu Biyu a Birnin Kaduna

Alamar Kotu.
Wata Mata Ta Kai Karar Tsohon Mijinta Gaban Kotun Musulunci Kan Cikin Da Take Dauke Da Shi Hoto: dailytrust
Asali: UGC

A jawabin lauyan mai ƙara, Abdullahi, ya gaya wa Kotu cewa:

"Muna kuma bukatar Kotu ta ba wacce ke ƙara izinin zuwa ta kwaso gado da kuma Teburin ajiya daga gidan tsohom mijinta da take ƙara."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

'N2,000 Kacal zan iya biya duk wata'

A ɓangarensa, wanda ake ƙara ta hannun lauyansa, Sadiq Marafa, yace ya saki matarsa ne saboda ta gudu daga gidan aurenta ba tare da izininsa ba.

Marafa yace:

"Wanda nake karewa na da masaniyar tana ɗauƙe da cikin wata biyar. Yana da karfin iya biyan N2,000 duk wata domin kula da cikin saɓanin N30,000 da take nema."
"Zamu ɗauki ɗawainiyar komai da kayan jariri da zaran ta kwanta naƙudar haihuwa."

Ya ƙara da cewa bai san komai game da wasu kayan ɗaki da suke mallakin matar ba, inda ya sanar da Alƙalin Kotun cewa bata zo da komai gidansa ba lokacin da aka ɗaura musu aure.

Kara karanta wannan

"Zamu Kawo Karshen Matsalar Tsaro Cikin Watanni Shida" Tinubu Ya Faɗi Matakan Da Zai Ɗauka

Bayan sauraron kowane ɓangare, Alƙalin Kotun mai shari'a Malam Rilwanu Kyaudai, ya ɗage zaman sauraron shari'ar zuwa 16 ga watan Nuwamba, NAN ta ruwaito.

A wani labarin kuma Bayan Mijinta Ya Gaza a Gado, Wata Mata Ta Faɗi Yadda Ya Gwada Kwazon Direbanta Har Ya Mata Ciki Sau 2

Wata matar aure ta fito ta bayyana yadda ta ci amanar Mijinta lokuta da dama a yunkurinta na ganin ta zama uwa.

A cewar wani Bidiyon da matar ta amsa laifinta, Matar ta ƙulla alaƙa mai ƙarfi da Direbanta kuma har ta haifi yara guda biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262