Da Duminsa: Gagarumar Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Tufafi ta Legas

Da Duminsa: Gagarumar Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Tufafi ta Legas

  • Mummunar gobara ta tashi a fitacciyar kasuwar tufafi dake Tejuosho a yankin Yaba dake jihar Legas inda yanzu ake kokarin kashewa
  • Duk da dai har yanzu ba a san musabbabin gobarar, ta lamushe runfuna masu tarin yawa inda take cigaba da maso shaguna na kusa
  • Har a lokacin rubuta wannan rahoton, jami’an hukumar kwana-kwana da ceto suna aikinsu sannan ba a san ko ta ci rai ko a’a ba

Legas - Jami’an hukumar kashe gobara a halin yanzu suna ta gwagwarmaya tare da kokarin kashe mummunar gobarar da ta tashi a kasuwar teloli dake bayan sabuwar kasuwar Tejuosho dake Yaba a jihar Legas.

Kasuwar Legas
Da Duminsa: Gagarumar Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwar Tufafi ta Legas. Hoto daga TheCable.com
Asali: UGC

Darektan Hukumar kashe gobara da ceto na jihar Legas, Margaret Adeseye ta tabbatar da faruwar lamarin kamaryadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya yi nadi mai muhimmanci, ya ba wani dan Katsina mukamin babban sakatare

Kamar yadda Adeseye tace, gobarar ta hada da wani bangare na kasuwar sutturu da kayan dinki wanda daga nan ta dinga cin runfunan dake kusa da ita.

A yayin rubuta wannan rahoton, ba a tabbatar da musabbabin gobarar ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gobarar dai ta fara ne a ranar Talata kuma ta lamushe gine-gine masu yawa a kasuwar kamar yadda jaridar TheCable ta rahoto.

Har a yanzu ba a san yawan rayukan da gobarar ta lamushe ba.

Jaridar TheCable ta tuntubi Nosa Okunbor, kakakin Hukumar kai agajin gaggawa na jihar Legas, kuma yayi alkawarin bada karin bayani kan aukuwar lamarin nan babu dadewa.

Karin bayani na tafe…

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng