Mbazulike Amechi, Ministan Sufurin Jiragen Sama Na Farko a Najeriya, Ya Rasu

Mbazulike Amechi, Ministan Sufurin Jiragen Sama Na Farko a Najeriya, Ya Rasu

  • Tsohon minista a Najeriya, Mbazulike Amechi ya riga mu gidan gaskiya bayan wata 'yar rashin lafiya karama
  • An ruwaito cewa, Mbazulike ne babban mai kare Nnamdi Kanu daga tsarewar da gwmanatin Najeriya ta Buhari ta yi masa
  • Majiyar dangi ta bayyana ranar da ya rasu, da kuma halin da ake ciki na jana'izarsa zuwa nan gaba kadan

Abuja - Ministan farko na ma'aikatar sufurin jiragen sama a Najeriya, Cif Mbazulike Amechi ya riga mu gidan gaskiya, rahoton The Nation.

A cewar wata majiyar dangi daga bakin Ezeana Tagbo Amechi na karamar hukumar Nnewi ta Kudu a jihar Anambra, tsohon dan siyasar ya rasu ne a yau Talata 1 ga watan Nuwamba da sanyin safiya.

Kara karanta wannan

Rasuwar dan Davido ta jawo jimami a PDP, jam'iyyar ta dakatar harkokinta na siyasa

Mbazulike Amechi ya riga mu gidan gaskiya
Mbazulike Amechi, Ministan Sufurin Jiragen Sama Na Farko a Najeriya, Ya Rasu | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Rahotannin da muke samu sun bayyana cewa, jigon na Kudu shine mutum na karshe da ya saura a tafiyar Zikist, kuma ya zama minista ne a lokacin yana da shekaru 29, ya rasu yana da shekaru 93.

An ce tsohon ministan ya bar garinsu mai suna Ukpor a jihar Anambra, inda ya koma Abuja zama tare da dansa a lokacin da jikinsa ya yi rauni, inji rahoton jaridar Vanguard ta da ta samo sanarwar da aka fitar ta rasuwar dattijon kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake raye, ya kasance daya daga cikin wadanda suka jagoranci tafiyar Inyamurai zuwa wurin Buhari domin ganin an sako shugaban kungiyar ta'addancin na ta IPOB, Nnamdi Kanu.

Najeriya ta yi rashi da yawa a shekarun nan, musamman na jiga-jigan siyasan jamhuriya ta farko.

Allah Ya Yi Wa Babban Malamin Addini A Najeriya Rasuwa

Kara karanta wannan

Matashi Musulmi Ya Auri Mata 'Yan Biyu A Rana Guda a Jihar Osun

A wani labarin, cocin Anglican, reshen jihar Legas, ta sanar da rasuwar Archbishop na Ecclesiastical Province na Legas, Most Rabaran Bamisebi Olumakaiye.

An sanar da rasuwar Most Rabaran Olumakaiye ne cikin wata takarda mai dauke da sa hannun sakatare, Ven. Segun Ladeinde; da Chancellor, Mai shari'a Adedayo Oyebanji, Channels TV ta rahoto.

Legit.ng ta tattaro cewa malamin addinin ya rasu a yammacin ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba yana da shekaru 53.

An nada Olumakaiye matsayin Bishop na Legas a ranar 30 ga watan Yulin 2018, a Nuwamban 2021 aka gabatar da shi matsayin Archbishop na Ecclesiastical na Legas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.