Matashi Musulmi Ya Auri Mata 'Yan Biyu A Rana Guda a Jihar Osun

Matashi Musulmi Ya Auri Mata 'Yan Biyu A Rana Guda a Jihar Osun

  • Yayinda aka samu wasu jaruman matasa masu auren mata biyu rana guda, an sabon salo mai ban mamaki
  • Wannan Matashi mata biyu yan gida daya kuma ya biyu ya aure ranar guda a yammacin Najeriya
  • Malaman addinin Islam sun yo tsokaci kan wannan lamari shin ya hallata ko kuwa bai halasta ba

Osun - Wani Mutumi dan garin Ede dake jihar Osun, Kudu Maso Yammacin Najeriya ya angwance da mata yan biyu ranar guda a karshen makon da ya gabata.

Wani dan jarida, Obarayese Sikiru, ya saki bidiyon daurin auren a shafinsa na Tuwita ranar 30 ga Oktoba, 2022.

Yace"

"Mutum ya auri yan biyu ranar Asabar a Ede, jihar Osun."
Obarayese
Matashi Musulmi Ya Auri Mata 'Yan Biyu A Rana Guda a Jihar Osun Hoto: @ObarayeseSikiru
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Ba Zamu Yarda Wani Dan Arewa Ya Gaji Buhari Ba: Kungiyoyin Kasar Yarbawa

A bidiyon, akan ji Malaman addini suna musu addu'an Allah ya basu zaman lafiya.

Wannan abu ya baiwa Malami mamaki shin ta yaya malamai suka amince akayi wannan daurin aure.

Wannan haramun ne, fadin Malamin addini

Legit ta tuntubi malamin addini kuma Limamin Masallacin Alhaji Bello Damagun dake unguwar Unguwar Asokoro Abuja.

Ya bayyana matsayar addini kan wannan aure da matashin yayi.

A cewarsa:

Wan nan Ya Aikata Haramun Don Ya sabawa Ayar Qur'ani Kai tsaye Cikin Fadin Allah A Surata 4 Ayata 22.
" (وان تجمعوا بين الأختين)
"Kuma Ku hada 'yan uwa 2 Lokaci Daya."
Wan nan Wani Yankine Na Ayar Dai Me Number ta 22 Cikin Surata 4 Kamar Yadda Yagabata Allah Yajero Matanda Yaharamta Mutum Ya,aura Har Yazo Nan Ga6ar .
Wallahu Aalam

Asali: Legit.ng

Online view pixel