Fashewar Tukunyar Gas Ta Halaka Wata Matar Aure a Jihar Kwara
- Wata Fashewar Tukunyar Gas da ake girki da ita ya yi sanadin mutuwar matar Aure da daren ranar Litinin a jihar Kwara
- Hukumar kashe gobara ta jihar, a wata sanarwa, tace jami'anta sun yi nasarar shawo kan lamarin cikin lokaci
- Shugaban hukumar ya shawarci mazauna su fara zuwa su koyi yadda ake amfani da Gas gabanin fara girki da shi a gida
Kogi - Fashewar tukunyar Gas ta halaka wata matar aure, Misis Adeola Adewale, a Egbe garage da ke yankin Omu-aran, ƙaramar hukumar Irepodun, jihar Kwara ranar Litinin.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 10:35 na dare lokacin da mamaciyar ke shirya wa iyalanta abincin dare.
Kakakin hukumar kwana-kwana ta jihar Kogi, Hassan Adekunle, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata (yau).
Adekunle ya ƙara da cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Fashewar Tukunyar Gas ta yi ajalin wata mata, Misis Adeola Adewale, ranar 31 ga watan Oktoba, 2022 a Anguwar Tebanacle 2c, Egbe Garage dake Omu-aran, ƙaramar hukumar Irepodun ta jihar Kwara."
"Mummunan lamarin mara daɗin ji da ya yi sanadin mutuwar matar ya faru ne da misalin ƙarfe 10:35 na dare yayin da take kokarin shiryawa iyalan gidan abinci."
"Jami'an mu sun yi namijin kokarin ɗaƙile lamarin a kan lokaci kuma suka tseratar da Mijin matar wanda fashewar ta rutsa da shi. Bugu da ƙari jami'ai sun yi saurin kai shi Asibiti domin samun kulawar da ta dace."
Bayanai sun nuna cewa wuraren da Fashewar Gas ɗin ta shafa sun haɗa da ɗakin girki, Falo da kuma Teburin cin abinci, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Hukumar kwana-kwana ta gargaɗi mata
Shugaban hukumar Kwana-Kwana ta jihar Kwara, Prince Falade John Olumuyiwa, ya gargaɗi ɗaukacin al'umma musamman mata su nemi ilimi kan amfani da Gas gabanin tunkararsa.
A wani labarin kuma Miji Ya Fadi Yadda Ya Kama Matarsa Dumu-Dumu Tana Saduwa da Dan Uwansa, Ya Nemi Saki a Kotu
Wani Magidanci ɗan kasuwa, Justine Onu, ya nemi wata Kotu a Abuja ta raba aurensa da Joyce bisa zargin ganinta ta kwanta da ɗan uwansa.
Mutumin ya faɗa wa Alkali cewa matar bata kula da shi, yayansa da sauran iyalai, burinta kawai ta kwanta kowa ta samu.
Asali: Legit.ng