Da Duminsa: Buhari Zai Shilla Birnin Landan Don Duba Lafiyarsa

Da Duminsa: Buhari Zai Shilla Birnin Landan Don Duba Lafiyarsa

  • Shugaba Muhammadu Buhari zai shilla birnin Landan inda zai bar babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja, a ranar Litinin
  • Kamar yadda mai bashi shawara na musamman kan yada labarai da hulda da jama’a, Femi Adesina ya bayyana, zai je duba lafiyarsa ne
  • Adesina ya sanar da cewa ana tsammanin Buhari ya dawo Najeriya a mako na biyu na watan Nuwamba bayan kammala duba lafiyarsa

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar birnin Abuja a ranar Litinin domin duba lafiyarsa a birnin Landan.

Buhari zai yi Tafiya
Da Duminsa: Buhari Zai Shilla Birnin Landan Don Duba Lafiyarsa. Hoto daga @BashirAhmaad
Asali: Facebook

Femi Adesina, mai baiwa shugaban kasan shawara na musamman a fannin yada labarai da hulda da jama’a ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Da Dumi: Shugaba Muhammadu Buhari Ya Dira Landan Don Ganin Likita

Yace ana tsammanin shugaban kasan ya dawo Najeriya a mako na biyu na watan Nuwamba.

Wannan ne karo na babu adadi da shugaban kasan ke shillawa ketare neman lafiya tun bayan hawa da mulki duk da yayi kamfen da inganta kiwon lafiya a 2015.

Duk da kasafta biliyoyin Naira kowacce shekara na asibitin dake gidan gwamnatin tarayya da sauran asibitocin kasar nan, shugaban Najeriyan da iyalansa sun saba shillawa ketare neman lafiya.

Duk da dai an bayyana cewa shugaban kasan asibiti zai je a London din, dama fadarsa bata bayyana wanne irin ciwo ke samun shugaban kasan ko a lokutan da ya kwashe watanni a ketare don jinya.

Shugaba Muhammadu Buhari Zai Shilla Kasar Koriya Ta Kudu Gobe

A baya kun ji cewa, Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi kasar Koriya ta kudu, nahiyar Asiya a gobe Lahadi, 23 ga watan Oktoba 2022.

Buhari zai dira birnin Seoul ne domin halartan taron ilmin hallita da rigakafi na duniya.

Kara karanta wannan

Rudani yayin da Gwamna El-Rufai ya yafewa wasu fursunoni hudu saboda wani dalili

Wannan shine karin farko da za'a shirya wannan taro.

Hadimin shugaba Buhari kam lamarin sadarwan zamani, Bashir Ahmed, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita.

A cewarsa, Buhari zai gabatar da jawabi a taron da aka shirya ranar 25 da 26 ga Oktoba.

A cewarsa:

“Shugaba Buhari gobe zai bar Abuja don zuwa Seoul, koriya ta kudu domin halartan taron ilmin halitta na duniya karon farko da gwamnatin Koriya da kungiyar lafiyan duniya ta shirya."
"Taron na kwana biyu (October 25-26), mai take "Rana goben rigakafi da ilmin halitta."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng