Binciken ‘Yan Majalisa Ya Bankado Yadda Biliyoyi Suka Bace a Ma’ikatar Tarayya
- Kwamitin majalisar dattawa yana binciken ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomin gwamnati a Najeriya
- Ana bincike na musamman a kan wasu kudi da ma’aikatu suka batar daga shekarar 2017 zuwa 2021
- Binciken ya soma nuna an fitar da fiye da N2bn da sunan ma’aikatar shari’a, amma babu labarin kudin
Abuja - Kwamitin binciken asusun kudin gwamnati ya gano Naira Biliyan 2.2 da ma’aikatar shari’a ta 'karba' a matsayin kudin ko ta-baci.
Tribune tace wannan kwamiti yana binciken ma’aikatun tarayya fiye da 200 domin gano gaskiyar inda Naira tiriliyan 5 suka shiga a Najeriya.
Ma’aikatun tarayya na da damar karbar kudi daga asusun Service Wide Votes (SWV). Ana amfani da wadannan kudi ne idan har matsala ta taso.
Kwanakin baya majalisar dattawa tace za ta binciki inda ma’aikatu suka kai wadannan kudi, an dauko aikin daga shekarar 2017 zuwa 2021.
Ba ayi bincike da kyau ba
Aikin kwamitin Sanata Mathew Urhoghide ya nuna Mai binciken kudin gwamnatin tarayya bai bi diddiki wajen binciken ma’aikatar shari’a ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Jaridar tace kwamitin majalisar dattawa da ke sa ido a kan aikin ma’aikatar kasar ba ta samu bayanin inda aka kai wadannan makudan kudi ba.
Da aka zauna domin wannan aiki, Sanatoci sun yi mamakin yadda ma’aikatar ta karbi wadannan kudi a 2019 da sunan kudin muhimman ayyuka.
An ware kudi daga OAGF
Bayanan da aka samu daga ofishin Akanta Janar ya nuna an ware N650m a karkashin kason kudin ayyuka, amma ma’aikatar ba karbi ko sisi ba.
Abin bai tsaya nan ba, OAGF ya warewa ma’aikatar irin wannan kudi har N955m a shekarar 2017, amma N549m aka tabbatar ya shiga asusun ma’aikatar.
Jaridar This Day tace a 2018, ma’aikatar tace ta karbi N492m, amma Akanta Janar yana ikirarin ya aiko N591m, a nan ma an samu gibin kusan N100m.
A 2020 da 2021, ma’aikatar ta karbi N62m da N400m, amma abin da aka fitar a OAGF a 2021 ya kai N1.4bn, majalisa ba ta san ina ragowar kudin suka shiga ba.
Da aka zauna da shi, Sakataren din-din-din na ma’aikatar ya shaidawa kwamitin zai dawo nan gaba domin yi masu bayanin yadda aka yi kasafin kudin.
Canza N200, N500 da N100
A ranar Asabar an ji labari Farfesa Kingsley Moghalu wanda ya yi aiki da Sanusi Lamido Sanusi II a CBN, ya yaba da batun buga sababbin takardun kudi.
Masanin tattalin arzikin ya kare Godwin Emefiele da ya ji Ministar kudin Najeriya ta caccaki matakin da bankin CBN ya dauka, yace hakan abu ne mai kyau.
Asali: Legit.ng