Yadda Mutum 306 Suka Samu Tagomashi Daga Kudin Zakkah, An Raba Masu N55m

Yadda Mutum 306 Suka Samu Tagomashi Daga Kudin Zakkah, An Raba Masu N55m

  • Kimanin mutum 306 ne suka samu tagomashi daga shirin rabon zakkah da kungiyar al’ummar Musulmi ta Lekki (LEMU) tayi a jihar Lagas
  • An rabawa mutanen da suka ci gajiyar shirin kayayyaki da tsabar kudi da yawansu ya kai naira miliyan 55
  • Wannan tsari an fito da shi ne da nufin kawar da talauci a tsakanin al'ummar kasar musamman duba ga yadda ake fama da tsadar rayuwa

Lagos - A kalla mutane 306 ne suka amfana daga shirin rabon Zakkah na kungiyar al’ummar Musulmi ta Lekki (LEMU) da ke jihar Lagas.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa kayayyaki da kudaden da aka rabawa wadannan bayin Allah ya kai kimanin naira miliyan 55.

An tara kudin ne daga sadaka da zakkah da ake karba don rabawa mabukata da nufin kawar da talauci.

Kara karanta wannan

2023: Abinda Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Tambayi Kowane Mai Burin Gaje Buhari, Dattawan Arewa

Rabon zakka
Kungiyar Lekki Ummah Ta Raba Kudin Zakkah Ga Mutane 306 a Legas Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Shugaban kwamitin karbar Zakkah da Sadaka na kungiyar LEMU, Alhaji Yunus Olalekan Saliu, ya bayyana cewa an samu karin wadanda suka amfana idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata inda mutum 226 ne suka amfana a lokacin da aka samu fiye da naira miliyan 60.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewarsa, karin mutanen da aka samu a wannan shekarar baya rasa nasaba da matsalar tattalin arziki da kasar Najeriya ke fuskanta inda a kullun darajar naira ke kara ruguzowa da kuma tsadar rayuwa wanda ya jefa mutane da dama a halin wayyo Allah.

Ya ce:

“Magana ta gaskiya it ace akwai kari a adadin mutanen da talauci ya yiwa katutu, da yaduwar yunwa da fusata a kasar nan.”

An raba wadanda suka amfana rukuni-rukuni inda mutum 261 suka samu tallafin N38.9m don kama sana’a, mutum 11 sun amfana a bangaren kiwon lafiya da naira miliyan 2.7.

Kara karanta wannan

Barazanar Tsaro: An Gano Asalin Dalilin Rudewa Amurkawa a Abuja

Sai mutum 18 da suka samu tallafin karatu da ya kai naira miliyan 4.2; mutum hudu sun samu an biya masu bashin N574,800, yayin da mutum 12 suka samu N2.1m na kudin haya.

Sauran kayayyakin da aka raba sun hada da manyan kulan sanyaya abun sha guda 50, keken dinky 20; injin nika uku, laftof biyu, janareto hudu; kamara daya da kuma injin din yin takalmi daya.

Da yake jawabi kan muhimmancin zakka, babban limamin masallacin Lekki, Sheikh Ridwan Jamiu, ya ce yana kawar da talauci da dinke Baraka tsakanin masu kudi da talakawa kamar yadda musulunci ta shardanta.

Raskwana: Fatima Adamu Maikusa, Yar Arewa Da Ta Lashe Gasar Lissafi Na Kasa da Kasa Har 7

A wani labari na daban, wata matashiyar budurwa yar Najeriya mai suna Fatima Adamu Maikusa, ta burge jama’a da dama saboda tarin baiwar da Allah yayi mata na iya lissafi sai kace na’ura mai kwakwalwa.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da NIA Sun Damke Yan Ta'addan ISWAP 35 A FCT Abuja

Fatima mai shekaru 14 ta kasance haifaffiyar yar jihar Gombe da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya.

An fara damawa da ita a gasar lissafi tun tana da shekaru tara a duniya inda ta fara da lashe gasar lissafi na Amurka (AMC 08).

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: