Yan Sanda Sun Dakile Hare-Haren Yan Bindiga, Sun Ceto Mutum 4 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara

Yan Sanda Sun Dakile Hare-Haren Yan Bindiga, Sun Ceto Mutum 4 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara

  • Yan sandan Zamfara sun yi nasarar dakile hare-haren yan bindiga a wasu kanannan hukumomin jihar
  • Jami'an yan sanda da ke faturol a wasu kauyukan jihar sun yi nasarar ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su
  • Kananan hukumomin da abun ya shafa sun hada da na Maru, Bungudu, Tsafe da Bukkuyum

Zamfara - Rundunar yan sandan Zamfara ta dakile hare-haren yan bindiga a kananan hukumomi hudu da ke jihar sannan ta ceto mutane hudu da aka yi garkuwa da su, jaridar Punch ta rahoto.

A wata sanarwa daga kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya ce yan bindigar sun so kai hari kan wasu kauyuka a kananan hukumomin Maru, Bungudu, Tsafe da Bukkuyum amma aka dakile shi bayan samun bayanan sirri.

Kara karanta wannan

Katsina: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 21 da ‘Yan Bindiga Suka Sace

Jami'an yan sanda
Yan Sanda Sun Dakile Hare-Haren Yan Bindiga, Sun Ceto Mutum 4 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Zamfara Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Shehu ya ce:

“Tsakanin Juma’a 28 da Lahadi 30 ga watan Oktoba, 2022, rundunar ta samu bayanan sirri kan shirin yan bindiga na kai hari wasu kauyuka a kananan hukumomin Bukkuyum, Tsafe, Bungudu, Gusau da Maru da nufin garkuwa da mutane.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Da samun bayanan, sai jami’an yan sandan suka shiga aiki da taimakon yan banga inda suka dakile hare-haren da kuma gudanar da faturol don kawar da duk wata barazana kan garuruwan."

Ya jadadda cewa kokarin yan sandan da yan bangan ya kuma yi sanadiyar ceto wasu mutane hudu da aka yi garkuwa da su, ciki harda dan shekara daya.

Shehu ya kuma bayyana cewa an ceto mutanen ne sakamakon bayanan da yan sanda suka samu kan sace su, inda aka bazama bincike da aikin ceto su kuma an yi nasarar kubutar da su cikin koshin lafiya.

Kara karanta wannan

An samu karin kasashe da suka gano yiwuwar kai hare-hare a Abuja da Jihohi 22

Jaridar Daily Post ta nakalto Shehu yana cewa:

“A yayin tattaunawa, mutanen sun sanar da yan sanda cewa a ranar 14 ga watan Oktoban 2022, yan bindiga da yawansu sun farmaki kauyen Kuraje a karamar hukumar Gusau sannan suka sacesu su hudu inda suka tisa keyarsu zuwa dajin Munhaye da ke karamar hukumar Tsafe inda suka shafe tsawon kwanaki 15 a tsare.
“An kwashi wadanda aka ceton zuwa asibitin yan sanda don duba lafiyarsu sannan daga bisani aka sadasu da yan uwansu."

Sojoji Sun Kama Kwamandan Yan Bindiga, Sun Kashe Mayaka 8 A Wata Jihar Arewa

A wani labarin kuma, dakarun rundunar sojojin sama da na kasa sun kashe wasu yan bindiga guda takwas yayin da suke yunkurin kai mummunan hari kan al'umma a jihar Neja.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa sojojin sun farmaki yan bindigar ne a lokacin da suke kokarin kaddamar da hari a New Bussa, karamar hukumar Borgu ta jihar Neja.

Kara karanta wannan

Gini Ya Danne Mutanen da Ambaliyar Ruwa Ta Raba da Gidajensu a Kogi, Rayuka Sun Salwanta

Majiyoyi daga garin sun bayyana cewa dakarun sojin hadin gwiwar sun kuma kama kwamandan yan bindigar wanda ya jagoranci kai harin a daren ranar Asabar, 29 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng