Rashin tsaro: Kayan yakin Najeriya Su na Kan Hanya daga Kasar Turkiyya inji Jakada

Rashin tsaro: Kayan yakin Najeriya Su na Kan Hanya daga Kasar Turkiyya inji Jakada

  • Hidayet Bayraktar ya yi albishir da cewa kayan yakin da Najeriya take sauraro daga Turkiyya za su iso
  • Jakadan na Turkiyya a Najeriya yace wannan yana cikin yarjejeniyar da aka yi alkawari a shekarar 2021
  • Kayan da za a aiko za su taimaka a yakar matsalar rashin tsaro da kuma fatattakar kungiyoyin ta’adda

Abuja - Jakadan kasar Turkiyya a Najeriya, Hidayet Bayraktar yace kayan aikin da aka saya domin magance matsalar tsaro su na daf da karasowa.

Daily Trust tace Hidayet Bayraktar ya yi wannan bayani a wajen bikin da kasar take yi a Abuja.

Jakadan kasar ya shaidawa jama’a cewa Turkiyya za ta ba Najeriya jirage marasa matuki da jirgi masu sukar ungulu kamar yadda aka yi alkawari.

Hidayet Bayraktar yace gudumuwar da kasarsa za ta ba Najeriya yana cikin nasarorin da aka samu a yarjejeniyar hadin-kan da aka shiga a 2021.

Kara karanta wannan

2023: Mutane Sun Fito Yayin da Ɗan Takarar AAC Ya Buɗe Kamfen Neman Gaje Buhari a Kano

Za mu taimakawa Najeriya - Turkiyya

An rahoto Jakadan yana mai cewa a shirye kasar Turkiya take wajen ganin ta taimakawa Najeriya ta yaki matsalar tsaro da fasahohin zamani.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Yarjejeniyar tsaron da kasashenmu suka shiga a shekarar bara ya bude sabon shafi.
Shugaban Kasar Turkiyya
Muhammadu Buhari da Shugaban Kasar Turkiyya Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Facebook

Bisa wannan dama, ina mai alfaharin bada sanarwar cewa wasu daga cikin kamfanonin tsaronmu Bayraktar (TB-2) da (T-149) ATAK za su zo Najeriya.

Bayraktar (TB-2) kamfani ne da yake kera jirage marasa matuki yayin da kamfanin (T-149) ATAK ya kware wajen aikin kera jirage masu saukar ungulu.

Kamar yadda The Cable ta kawo rahoto, kayan aikin za su taimakawa gwamnati da mutanen Najeriya wajen inganta tsaro da ganin an kawo zaman lafiya.

Alakar kasashen 2 tana kara kyau

Har ila yau, Jakadan kasar yace yana sa ran gwamnatin Najeriya ta maida alheri ta hanyar yakar duk kungiyoyin ta’adda na FETO da ke zama a kasar nan.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu, Obi ko Atiku? Bincike Ya Nuna Wanda Zai Ci Zaɓen Shugaban Ƙasa, An Bayyana Abin Da Zai Faru

Karamin Ministan harkokin kasar waje, Amb. Zubairu Dada yace alakar da ke tsakanin kasashen ta karu sosai musamman bayan zaman da aka yi a 2021.

Matsalar tsaro a Najeriya

Da sanyin asubar Juma’a aka ji labari miyagun ‘yan bindiga sun aukawa wani kauye da ke karkashin garin Zurmi a Zamfara, sun dauke Mai garin da kaninsa.

‘Yan bindiga sun yi hakan ne domin nuna fushinsu saboda an karbe masu babura. Mun ji labari cewa sun bukaci a biya fansar N5m, kuma a dawo da baburan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng