Da Duminsa: FG Ta Nisanta Kanta da Batun Sauya Wasu Takardun Naira
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa bata da masaniya ko kadan kan batun sauya wasu daga cikin takardun kudin kasar nan da CBN ta bayyana zata yi
- Kasa da sa’o’i 48 da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele ya bayyana sabon tsarin, Ministan kudi Zainab Ahmed tace a kafafen yada labarai suka tsinta lamarin
- A cewarta, ba zata iya tsokaci kan muhimmacin sauya kudin ba ko akasin hakan a wannan lokacin ba, amma majalisa ta gayyaci Emefiele don karin bayani
FCT, Abuja - Kasa da sa’o’i arba’in da takwas bayan Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya sanar da cewa bankin zai sauya wasu daga cikin kudaden kasar a ranar 15 ga watan Disamban 2022, gwamnatin tarayya a ranar Juma’a tace bata amince da hakan ba.
Ministan kudi, kasafi da tsari, Zainab Ahmed tace bata amince da tsarin ba inda tace in har aka tabbatar da shi za a samu babbar matsala a kasar da tattalin arzikinta.
Zainab wacce tayi tsokaci kan tsarin a yayin martani ba tambayar da Sanata Opeyemi Bamidele yayi yayin kare kasafin kudi na 2023, ta ja kunnen babban bankin kan matsalolin da ka iya tasowa.
Sanata Bamidele wanda a tambayarsa ya sanar da ministan cewa kasa da kwanaki biyu da sanar da tsarin, an fara jin illarsa kan darajar Naira idan aka danganta ta da dala.
Yace:
“Kwanaki biyu kacal da sanar da tsarin, darajar Naira idan aka danganta ta da dala tayi kasa. Dala daya rana da darajar N740 zuwa N788 sakamakon kokarin da ake wurin ganin an canzata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“A gani na, wannan tsarin mai kyau ne amma lokacin ne ba daidai ba saboda naira zata iya faduwa har ta kai N1,000 kafin ranar 31 ga watan Janairun 2023 da aka tsayar don tabbatar da tsarin.”
Vanguard ta rahoto cewa, yayin amsa tambayarsa, ministan tace bata san da tsarin ba sai dai kawai ta ji shi a kafar sada zumunta.
Tace:
“Masu girma sanatoci, ba a tuntubi ma’aikatar kudi ba kan sake wasu takardun Naira kuma ba zan yi tsokaci kan amfanin hakan ko akasinsa ba.
“”Sai dai a matsayinmu na ‘yan Najeriya da suka samu damar kasancewa a matakin sama na fannin, akwai yuwuwar illa mai yawa kan darajar Naira idan ta tabbata.
“Sai dai zan yi kira ga wannan kwamitin da yayi kira ga gwamnan bankin domin samun bayanan da suka dace a fannin amfanin tsarin da daidan shi ko akasin hakan.”
Dalilin Da Yasa CBN Zata Sauya Wasu Takardun Kudaden Najeriya
A wani labari na daban, a wani yunkuri da ta sanar matsayin mataki na yaki da ayyukan ta’addanci, boye kudade da kuma yaki da kudin jabu, babban bankin Najeriya (CBN) ya ce zai fara rarraba sabbin takardun N100, N200, N500 da kuma takardar N1000 daga ranar 15 ga Disamba.
Gwamnan babban bankin kasa, CBN, Godwin Emefiele, wanda ya bayyana hakan a jiya yayin wani taron tattaunawa na musamman ya ce za a sake fasalin kudin Naira ne bayan amincewar gwamnatin tarayya, Daily Trust ta rahoto hakan.
Asali: Legit.ng