Kada A Saki Nnamdi Kanu, Kotun Daukaka Kara Ta Yanke Sabon Hukunci
- Bayan nasarori biyu da ya samu kan gwamnati a baya, Nnamdi Kanu ya sake fuskantar cikas ga yancinsa
- Kotun daukaka kara ta ce kada a sake shi sai kotun koli ta yanke shawarar karshe kansa
- Gwamnatin Buhari a shekarar 2021 ta sankamo Nnamdi Kanu daga kasar Kenya inda ya tafi harkoki
Kotun daukaka kara a ranar Juma'a ta amince da bukatar gwamnatin tarayya na hana aiwatar da dokar babbar kotun tarayya ta ranar 13 ga Oktoba cewa a saki Nnamdi Kanu.
Alkali Haruna Tsammani wanda ya yanke hukuncin ya bada umurnin cewa a tafi kotun koli cikin kwanaki bakwai don a yanke hukuncin karshe, rahoton ChannelsTV.
Hakan na nufin cewa za'a cigaba da rike Nnamdi Kanu a magarkamar hukumar tsaron farin kaya DSS har sai kotun kolin ta yanke hukunci.
Alkalin yayin yanke hukunci yau yace takardar da lauyoyin Kanu suka shigar don kawar da gwamnatin tarayya ba su kamshin gaskiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu Ta Umurci Gwamnatin Tarayya Ta Biya Nnamdi Kanu N500m Kuma A Mayar Da Shi Kenya
Babbar kotun tarayya dake zamanta a Umuahia, jihar Abia ta umurci gwamnatin tarayya ta mayar da Nnamdi Kanu inda suka dauko shi a kasar Kenya a watan Yunin 2021.
Nnamdi Kanu shine shugaban kungiyar masu rajin kafa kasar Biafra IPOB.
Bugu da kari, kotu ta umurci gwamnati ta biya Kanu kudi N500 million a matsayin garkuwa da shi da gwamnati tayi da kuma take masa hakki na bil adama.
Kotu Ta Wanke Nnamdi Kanu Amma Bata Ce Mu Sakeshi ba, AGF Malami
Antoni-Janar na tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, a ranar Alhamis ya yi tsokaci kan hukuncin kotun daukaka kara da ta wanke Nnamdi Kanu.
Nnamdi Kanu shine jagoran kungiyar rajin kafa kasar Biyafara watau IPOB.
A jawabin da mai magana da yawunsa, Dr. Umar Jibril Gwandu, ya fitar, Mr Malami ya ce kawai kotu ta wanke Kanu ne amma bata ce a sakeshi
Yace:
"Ofishin Antoni Janar na tarayya kuma Ministan Shari'a ta samu labarin kotun daukaka kara game da Nnamdi Kanu."
"Amma fa a sani, kawai an wanke Kanu ne amma ba'a sake shi ba."
Asali: Legit.ng