Ba Sojojin Amurka Ne Suka Kai Samame A Abuja Ba, In Ji Mazaunin Unguwa
- Wani mazaunin unguwar Trademore Estate a birnin tarayya Abuja ya ce ba sojojin Amurka ne suka kai samame ba a unguwar
- Mazaunin unguwar da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa jami'an DSS ne kimanin 30 sai farin fata daya kacal
- A bangarensu, rundunar yan sandan Najeriya da hukumar DSS sun karyata rahoton cewa an gano abin fashewa a unguwar ta Trademore
Abuja - Sojojin Amurka ba su cikin wadanda suka kai samame a rukunin gidaje na Trademore da ke Lugbe, babban birnin tarayya, Abuja, in ji wani mazaunin unguwar, Daily Trust ta rahoto.
Mazaunin, wanda ya tabbatar an kawo samame unguwar, ya ce kawai dan kasar waje daya aka gani cikin jami'an da suka kawo samamen.
Yan sanda da DSS sun karyata rahoton gano abn fashewa a Abuja
A hirar da ya yi da Daily Trust a ranar Laraba, kakakin yan sandan Abuja, Josephine Adeh, ta ce mazauna unguwar ba su sanar da rundunar game da lamarin ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adeh, mataimakiyar sufritandan yan sanda, kuma ta ce 'labarin karya ne' rahoton da ke ikirarin jami'an DSS da sojojin Amurka sun gano akwatunan abubuwa masu fashewa a unguwar.
Ta ce:
"Ina tuntubar DPO na unguwar, hakan bai faru ba. Babu wani abu a teburin DPO da ya ce mazauna unguwar sun kai wa yan sanda rahoton faruwan abin da ake ikirari."
Amma, ta umurni wakilin Daily Trust ya tuntubi DSS don karin haske.
An kira kakakin na DSS sau da yawa a ranar Laraba amma bai amsa kiran ba.
Amma, daga bisani a ranar Alhamis ya ce rahoton 'labarin karya ne'.
Ba sojojin Amurka suka kawo samame ba, farar fata daya tak muka gani - Dan Unguwar Abuja
Amma, wani mazaunin unguwar wanda ya nemi a boye sunansa ya ce an kama mutum biyu da ake zargi kusa da cocin Living Faith a unguwar.
Wani mazaunin ya ce jami'an sun kusa 30.
Ya ce:
"Wasunsu sun saka takunkumin fuska; dukkansu ba su saka unifom ba; mutum daya kacal ne farar fata' watakila hakan yasa aka yi tunanin sojan Amurka ne."
"Lokacin da jami'an tsaron suka iso, ba su iya gano wadanda suke nema cikin sauki ba. Sun rika gida-gida suna matsawa mutane. Ba su bari wani ya kusance su ba. Daga baya ne suka gano wadanda ake zargin suka tafi da su."
Jami'an DSS da NIA Sun Damke Yan Ta'addan ISWAP 35 A FCT Abuja
Hukumar tsaron farin kaya DSS, hukumar leken asirin Najeriya NIA, yan sanda da sauran jami'an tsaro sun kai harin kwantan bauna kauyukan Abuja kuma sun yi babban kamu.
Punch ta ruwaito cewa jami'an tsaron sun garkame kwamandojin ISWAP biyar da mayaka 30 a unguwanni irinsu Mararaba dake makwabtaka da ke kwaryar birnin tarayya Abuja.
Rahoton ya kara da cewa suna tsare yanzu a ofishin DSS.
Asali: Legit.ng