Zargin Safarar Sassan Bil Adama: An Bukaci Birtaniya Ta Saki Ekweremadu Da Matarsa
- Wata kungiyar yan Najeriya sun roki gwamnatin Birtaniya ta bada belin Sanata Eke Ekweremadu da matarsa Beatrice
- An kama tsohon mataimakin shugaban majalisar ne da matarsa kan zargin safarar sassan jikin bil adama watanni da suka shude
- Paul Sawa, shugaban kungiyar ya bayyana karkashin doka duk wanda ake zargi ba mai laifi bane har sai an tabbatar da laifin
FCT, Abuja - Wasu yan Najeriya wadanda abin ke damunsu, sun roki gwamnatin Birtaniya ta bada belin tsohon mataimakin shugaban majalisar Najeriya, Ike Ekweremadu da matarsa, Beatrice, Daily Trust ta rahoto.
Sunyi wannan rokon ne karkashin wani kungiya mai suna 'Concerned Nigerians United for Ekweremadu and Family'.
Ana zargin cewa mata da mijin sun yi safarar wani matashi dan shekara 21 zuwa Birtaniya don cire kodarsa su bawa yarsu.
Ekweremadu mutum ne mai halayen dattaku da taimakon al'umma - Paul Sawa
Da ya suke magana a Abuja a ranar Alhamis, kungiyar Concerned Nigerians United for Ekweremadu and Family, sun bayyana Ekweremadu a matsayin mai biyayya ga doka, mai halayen dattaku kuma mai tallafawa al'umma wanda ya yi amfani da arzikinsa don tallafawa talakawa da sauran mutanen yankinsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Shugaban kungiyar, Paul Sawa, ya ce bisa adalci irin na doka, duk wani da ake zargi da laifi, ana daukansa mai gaskiya ne har sai an tabbatar da laifinsa a gaban kotu.
Sun kara da cewa a yayin da ba su shakkan cewa daga karshe za a gano Ekweremadu ba shi da laifi kuma a sake shi, 'suna tunatar da cewa jinkirta adalci, rashin adalci ne.'
Zargin Cire Koda: Da Alamu Ekweremadu Zai Dade A Gidan Yari, An Samu Sabon Cigaba
Tunda farko, David Ukpo, wanda ake zargin an kai shi Landan don cire masa koda, ya roki babban kotun tarayya ta janye hukuncin da ta yi na tura bayanansa zuwa Landan don cigaba da shari'ar Sanata Ike Ekweremadu da matarsa Beatrice.
Wani rahoto na Jaridar The Nation ta ce Ukpo, ta bakin lauyansa Bamidele Igbinedion ya koka cewa ba a saka shi ko Antonji Janar na Najeriya ba cikin karar da ya yi sanadin hukuncin na ranar 1 ga watan Yuli da Mai Shari'a Inyang Ekwo ya fitar.
Asali: Legit.ng