Wani Saurayi da Budurwa ýan damfara sun shiga hannu a kasuwar kantin kwari
Rundunar Yansandan jihar Kano ta sanar da damke wasu yan damfara da suka addabi kasuwannin jihar Kano, a ranar Talata, 7 ga watan Nuwamba.
Wadannan yan Damfara, da suka hada da Saurayi da Budurwarsa na amfani da wani sakon karta kwana na bogi ne, inda suke damfarar yan kasuwa da nufin zasu biya su kudin cinikinsu, amma sai su aika musu wannan sakon bogi.
KU KARANTA: Yan taya ɓera ɓari: Wasu Ýansanda dake safarar tabar wiwi buhu 30 sun shiga hannu
Mutanen sun hada da Jessy da Jennifer, kuma asirinsu ya tonu ne yayin da suka afka shagon wani mai siyar da atamfofi a kasuwar, inda suka siya kaya, kuma suka bukaci a basu lambar asusun banki don su biya kudin.
Legit.ng ta ruwaito da aka basu lambar asusun banki na UBA, sai suka ce ba yayi, haka dai aka dinga basu lambobi daban daban, sai suce baya yi, daga karshe aka samu wani lama da kyar, inda Jessy ya fara tura musu naira 5,000.
Sai dai yaron shagon yayi basira, inda yace a bashi damar yaje ya duba asusun bankin nasa ta ATM, don ya tabbatar 5,000 din ya shiga, haka kuwa aka yi, daya duba ya gani, sai ya fada ma Maigidansa, sai suka bukaci Jessy ya biya su kudin kayan, inda ya aika masa da kimanin N150,000, amma da yaron ya duba sai bai gansu ba.
Ana cikin haka ne sai wani mutumi da suka taba damfararsa ya shigo shagon, ganinsu ke da wuya ya kwarmata ihu, yana ihun barayi! Nan da nan aka kama su aka mika ma Yansanda.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
DUBA NAN: Jaridar Legit.ng Hausa ta kawo maku hanya mafi sauki da zaku iya karanta labaranta
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng