Zargin Damfarar N109bn: EFCC Ta Sake Gurfanar Da AGF Idris Da Aka Dakatar Da Wasu

Zargin Damfarar N109bn: EFCC Ta Sake Gurfanar Da AGF Idris Da Aka Dakatar Da Wasu

  • Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta sake gurfanar da Ahmed Idris, dakataccen akanta janar da wasu mutum uku kan zargin badakalar N109.5 biliyan
  • A wannon karon ma dukkan mutane ukun da ake tuhuma da almundahar kudaden sun musanta aikata hakan
  • Lauyan Idris da sauran wadanda ake tuhuma sun nemi kotun ta cigaba da basu beli, ta amince da hakan ta zabi ranar cigaba da shari'a

Abuja - Hukumar yaki da rashawa, EFCC, a ranar Laraba ta sake gurfanar da dakataccen Akanta-Janar na Tarayya, Ahmed Idris da wasu mutum uku kan zargin damfara ta N109.5 bn a babban kotun Maitama Abuja.

Sauran wadanda aka gurfanar sune Olusegun Akindele; Mohammed Usman da Kamfanin Gezawa Commodity and Exchange Limited, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Karo Na Biyu: Kotu Ta Sake Yi Wa Mama Boko Haram Ɗaurin Gidan Yari Kan Zambar Maƙuden Miliyoyin Naira

idris
Zargin Damfarar N109bn: EFCC Ta Sake Gurfanar Da AGF Idris Da Aka Dakatar Da Wasu. @AriseTv.
Asali: Twitter

An fara gurfanar da su ne a ranar 22 ga watan Yuli gaban Mai shari'a Adeyemi Ajayi kan tuhuma 13 masu alaka da almundaha na kudi har N109.5 biliyan kafin ya tafi hutu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma bayan kotun ta dawo zamanta, an mika shari'ar zuwa ga Mai shari'a Yusuf Halilu.

Wanda ake zargin sun musanta tuhumar da ake musu, kotu ta sake basu beli

Dukkansu sun musanta tuhumar da hukumar EFCC ke musu.

Bayan musanta aikata laifukan, lauyan Idris, Chris Uche, SAN, ya roki kotu ta bawa wadanda ake tuhumar dama su cigaba da morar belin da aka basu tunda farko a ranar 28 ga watan Yuli.

Ya ce sun kasance suna bin dokokin belin.

Lauyoyin da ke kare sauran mutanen uku sun bi sahunsa wurin neman belin.

Lauyan EFCC, Oluwaleke Atolagbe, bai yi jayayya da neman belin ba.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin daka tsige DPO daga kujerarsa bisa zargin kashe dan bindiga

Da ya ke yanke hukunci, Mai sharia Halilu ya ce beli hakki ne na wadanda ake tuhumar.

Ya ce tunda an taba basu belin a baya, shima zai kyallesu su cigaba da morar belin.

Amma, ya umurci wadanda ake tuhumar su mika fasfo dinsu na kotu.

Alkalin ya dage cigaba da sauraron shari'ar zuwa ranar 23 ga watan Nuwamba.

Zargin da EFCC ke musu

EFCC ta yi zargin cewa tsakanin Fabrairu da Disamban 2021, Idris ya karbi rashawa daga Akindele na kudi N15.1 biliyan don gaggauta biyan kashi 13 na ribar man fetur ga jihohin da ke samar da mai, ta hannun ofishin akanta janar.

Hukumar yaki da rashawar ta kuma ya zargin cewa wadanda ake zargi na faro da na biyu sun karkatar da N84.3 biliyan daga asusun gwamnatin tarayya.

EFCC ta ce laifukan sun saba da sashi na 155 da 315 na Penal Code Act Cap 532 na dokokin tarayyar Najeriya, 1990.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Bindiga Suka Sace Mutum 13 Yayin Kazamin Harin Da Suka Kai Wani Kauye A Neja

Wadanda ake tuhumar sun musanta aikata laifukan.

EFCC Ta Gurfanar Da Dakataccen Akanta Janar Na Tarayya A Gaban Kotu Kan Zambar N109bn

Tunda farko, Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta isa babbar kotun tarayya tare da dakataccen Akanta Janar na tarayya, Ahmed Idris, jaridar The Cable ta rahoto.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa tsohon Akanta Janar din da wasu biyu sun gurfana a gaban kotun da ke Abuja a yau Juma’a, 22 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164