Alaka Ta Da Buhari Itace Ta Gaskiya, Kuma Abin Koyi, Inji Osinbajo

Alaka Ta Da Buhari Itace Ta Gaskiya, Kuma Abin Koyi, Inji Osinbajo

  • Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bayyana kadan daga alherin da ya samu a kasancewarsa da shugaba Buhari
  • Ya bayyana cewa, alakarsa mai karfi ce da Buhari, kuma tabbas alakarsu abin koyi ne mai cike da darasi
  • Watanni kadan ya rage shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo su sauka daga kujerunsu

Jihar Kano - Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya yaba da irin alakar dake tsakaninsa da uban gidansa shugaba Muhammadu Buhari, tare da kwatanta alakar da cewa sahihiyace kuma abin koyi.

Osinbajo ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin kaddamar wani littafin gwamna Ganduje na jihar Kano, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Osinbajo ya fadi dangartakarsa da Buhari
Dangantaka Ta Da Buhari Itace Ta Gaskiya, Kuma Abin Koyi, Inji Osinbajo | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Ya kuma bayyana dalilin da yasa shugabannin siyasa da mataimakansu ke gina sahihiyar alaka a tsakanin juna.

Mataimakin shugaban kasan ya kuma bayyana cewa, shi dai ya fi sauran mataimakan sa'ar samun uban gida.

Kara karanta wannan

Musulmi da Kirista duk daya ne: Tinubu ya yiwa malaman addini jawabi a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Buhari ya sake wa Osinbajo ya yi aiki tukuru

Wata sanarwa da mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande ya fitar, ta ce:

"Da yake bayyana alakar dake tsakaninsa da mai gidansa - shugaban kasa Muhammadu Buhari ya siffanta ta da sahihiya kuma abin koyi, mataimakin shugaban kasan ya ce 'na yi sa'a fiye da saura a alakata da mai gida na, shugaban kasa.
"Lokacin da ya yi tafiyar rashin lafiya, a karo na biyu, akwai abubuwan da ya kamata a tura masa, amma ya ce 'bana bukatar ka tura min komai, aikinka ne yanzu, kawai ka tabbata ka yi aiki mai kyau."

Hakazalika, da yake kwatanta alakarsa da Buhari, ya ce kamar dai direbobin jirgi ne dake tafiya a jirgi guda daya.

Hakazalika, ya yada a shafinsa na Twitter cewa:

Kara karanta wannan

Osinbajo Ya Zauna da Hadimansa, Ya Fada Masu Wanda Za Su Marawa Baya a Zabe

"Rike ofishin gwamnati aiki ne na samun damar yin hidima da kuma taba rayukan miliyoyin jama'a, a madadin abubuwa masu dadi dake tattare da ofishin."

Zan Yi Kamfen da Lambar Yabon da Shugaba Buhari Ya Bani, Inji Gwamnan PDP Wike

A wani labarin, gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya bayyana cewa, zai yi amfani da lambar yabon da shugaban kasa Muhammadu ya bashi wajen yakin neman zaben 2023, Punch ta ruwaito.

Wike ya bayyana hakan ne a wani taron nuna lambar yabon da Buhari ya bashi, wanda aka gudanar a babban birnin jiharsa, Fatakwal a daren jiya Litinin 24 ga watan Oktoba.

Yayin da yake sadaukar da lambar yabon ga ubangiji, ya kuma shaida cewa, gwamnatinsa ta samu nasarar yin ayyukan more rayuwa ne saboda kwarin gwiwar da yake samu daga mutanen jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.