Zaben 2023: Jerin Jihohin Da Kwankwaso Da Obi Basu Da Rundunar Yakin Neman Zabe
- Duk da shaharar Peter Obi na jam'iyyar LP da Kwankwaso na NNPP, sai sun yi da gaske a zaben 2023
- Kwankwaso da Peter Obi basu da yan takara a wasu jihohi biyar da mazabun Sanata kimanin 20
- Hakan ya sa basu da rundunar yakin neman zabe a lunguna da sakon wadannan jihohi
Yan Najeriya musamman matasa na yunkurin tunkude jam'iyyun All Progressives Congress APC da People's Democratic Party PDP a zabukan da zasu gudana a 2023.
Cikin kankanin lokaci, dan takaran jam'iyyar Labour Party LP, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), sun samu karbuwa wajen yan Najeriya.
Amma a yanzu da zabe ya kusanto, wadannan yan takaran biyu basu da yan takaran gwamna a wasu jihohi.
"Ku Yi Hattara Da Mayaudaran Ƴan Siyasa", APC Ta Aikewa Ƴan Najeriya Sako Mai Ƙarfi A Gabanin Zaɓen 2023
Yayinda LP ba tada dan takaran gwamna a jiha 1, NNPP ba tada dan takaran gwamna a jihohi 4.
Jam'iyyar Labour Party dan takara a jihar Ogun, yayinda NNPP ba tada dan takara a Borno, Cross River, Kebbi da Zamfara.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Basu da yan takaran Sanata sama da 20
Wadannan jam'iyyu biyu basu da sojojin yakin neman zabe a wadannan mazabu saboda rashin isassun mambobi.
A zaben majalisar dattijai, Labour Party ba tada yan takara a mazabu 28 cikin 109.
A majalisar wakilai kuwa, NNPP ba tada yan takara biyu cikin 360 yayinda LP na tada yan takara a mazabu 128.
Ga jerin mazabun da basu da yan takara:
Bauchi Ta Arewa;
Bayelsa Ta Gabas
Bayelsa Ta Yamma
Mazabun Borno 3
Delta ta Arewa
Delta ta tsakiya;
Mazabun Ekiti 3;
Jigawa South West
Jigawa North West;
Mazabun Katsina 3,
Mazabun Kebbi 3;
Kogi West;
Mazabun Lagos 3;
Niger North;
Ondo Central
Ondo South;
Sokoto North,
Yobe North
Yobe East.
Asali: Legit.ng