Karo Na Biyu: Kotu Ta Sake Yi Wa Mama Boko Haram Ɗaurin Gidan Yari Kan Zambar Maƙuden Miliyoyin Naira
- Kotu a Maiduguri ta yanke wa Aisha Alkali Wakil (Mama Boko Haram) da wasu mutane biyu hukuncin daurin gidan yari kan zambar N34m
- Wilson Uwujaren, mai magana da yawun hukumar EFCC ce ta bayyana hakan cikin sanarwar da ta fitar a ranar Litinin
- Mai shari'a Kumaliya, yayin hukuncin ta yi wa mutanen uku daurin shekara 12 ba tare da zabin biyan tara ba
Borno - Babban kotun tarayya da ke Maiduguri, jihar Borno ta yanke wa Aisha Alkali Wakil, wacce aka fi sani da Mama Boko Haram, da wani Tahiru Saidu-Daura da Lawal Shoyode hukuncin daurin gidan yari.
Hakan na zuwa ne bayan da hukumar yaki da rashawa, EFCC, reshen jihar Borno ta gurfanar da wadanda aka yanke wa hukuncin a kotu kan laifuka uku na hadin baki da zamba na kudi N34,593,000.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sanarwar da mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren ta fitar ya ce:
"Yayin yanke hukuncin a yau, Mai shari'a Kumaliya ta samu wadanda aka yi karar da laifuka uku kuma aka yanke musu hukunci."
A cewar alkalin:
"A laifin farko na hadin baki, kotun ta yanke musu muku, Aisha Alkali-Wakil, Tahiru Saidu Daura da Prince Lawal Shoyode daurin shekaru biyar ba bu zabin tara.
"Yayin da a laifi na biyu da uku, Aisha Alkali-Wakil da Tahiru Saidu Daura za su tafi gidan yari na shekaru bakwai ba tare da zabin tara ba."
Ta kuma ce kotu ta umurci Wakil ta biya N25,805,000 ko ta tafi gidan yari na shekaru bakwai, yayin da Daura kuma zai biya N8,788,000 ko ya tafi gidan yari na shekaru bakwai.
Ta kara da cewa:
"Wakil da Daura tare za su biya N7,184,250 na kayan da aka kai musu ofishinsu ko kuma su tafi gidan yari na shekaru uku kowannensu."
Kotu Ta Yanke Wa 'Mama Boko Haram' Daurin Shekaru 5 Kan Damfarar N71.4m
A baya, babban kotu a jihar Borno ta yanke wa Aisha Wakil da aka fi sani da 'Mama Boko Haram' hukuncin daurin shekaru biyar a gidan gyaran hali kan damfara.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da hukumar EFCC ta wallafa a shafinta a daren ranar Talata.
Asali: Legit.ng