Bankin Musulunci Zata Baiwa Najeriya sama da N786b, Ta Nemi Alfarma Daya
- Najeriya zata samu $1.8 biliyan daga bankin Musulunci domin habaka ababen more rayuwa a fadin kasar nan da manyan ayyuka
- Bankin Musuluncin ya bayyana shirinsa na tamfatsa babbar hedkwatarsa a Najeriya kuma tana son daukin gwamnatin tarayya
- Bankin Cigaban Musuluncin yana da rassa 57 a kasashe a fadin duniya inda Najeriya ke rike da kashi 8.75 cikin dari na daidaito
FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayyar Najeriya zata samu $1.8 biliyan daidai da N786.60 biliyan daga bankin cigaban Musulunci.
Shugaban bankin Saudin, Dr Mohammed Jasser ya bayyana hakan a ganawar da suka yi da ministan kudi, kasafi da tsari na kasa, Zainab Ahmed, a Abuja a ranar Litinin.
Kamar yadda bankin ya bayyana, kudin za a yi amfani da shi wurin aiwatar da manyan ayyuka a fadin kasar nan.
“Bankin Cigaban Musulunci ya amince da bai wa Najeriya $1.8 biliyan.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Wannan ya hada da $972 miliyan na daukar nauyin ayyuka da $288 miliyan na wurare masu zaman kansu da $477 miliyan ta cinikayya wacce ta fito daga bangaren cinikin makamai da sauransu.”
Yace ayyukan bankin sun shiga da kasashe goma sha biyar kuma ya yabawa gwamnatin tarayya kan fadada bangaren tattalin arziki da yayi.
“Bankin Musuluncin zai taimakawa Najeriya wurin farfadowa daga illar annobar Korona wacce ta hada da taimakon dole a bangarori masu zaman kansu zuwa samar da ayyukan yi da farfado da tattalin arziki.
Ya bayyana manyan ayyuka biyu da suka hada da:
- Special Afro Industrial Processing Zones
- The Nigeria-Morocco gas Pipeline.
Inda yace bankin ta san da cigaban da ake samu da damammakin da Najeria ke bayarwa a bangarorin ma’aikatu masu zaman kansu.
Bukatar gina hedkwata a Najeriya
Jaridar ThisDay ta rahoto cewa Jasser yayi roko ga ministan da ta taimakawa bankin wurin samun wuri inda zata iya a Abuja domin gina katafaren ofishin bankin saboda na yanzu yayi mu kadan.
Yace bankin yana da shirye-shirye manya uku a Najeriya da ya hada da daya a hukumar Hajji ta Najeriya domin taimakawa kasar.
Jerin Kasashe 5 da Suke Bin Najeriya Bashi da Zunzurutun Kudaden da Suke bi, China ce Kan Gaba
A wani labari na daban, kamar yadda bayanan da aka samu daga ofishin kula da basussuka, kasashen duniya biyar ne ke bin Najeriya zunzurutun kudi har $4.49 biliyan wanda yayi daidai da N1.91 tiriliyan idan aka canza dala kan N430 a watan Maris na 2022.
Kasashen da Najeriya ta dinga rancen kudi cikin shekarun nan sun hada da Faransa, China, Japan, Indiya da Jamus.
Asali: Legit.ng