Akwa Ibom Ta Ce Jihar da Ta Fi Kowacce Tsafta a Najeriya, ta Fito a Afrika

Akwa Ibom Ta Ce Jihar da Ta Fi Kowacce Tsafta a Najeriya, ta Fito a Afrika

  • Jihar Akwa Ibom ce jihar da ta tafi kowacce jiha tsafta a Najeriya, kuma haka nan ta fito a jerin jihohi mafi tsafta a nahiyar Afrika
  • Kasar mai arzikin man fetur dai tana Kudu maso Kudancin Najeriya ne, kuma ba kanwar lasa bace wajen kasancewa tsaf-tsaf da kwalliya
  • A cikin shekaru hudu da suka gabata, jihar Akwai IIbom ce ke fitowa a matsayin jihar da ta fi kowacce jiha tsafta a fadin Najeriya ba tare da hamayya ba

Akwa Ibom - An ayyana jihar Akwai Ibom a matsayin jihar da ta tafi kowacce a jihohin Najeriya tsafta, kana daya daga cikin masu tsafta a Afrika, inji rahoton Daily Trust.

A cikin jerin da kafar yanar mai tasiri, ta duba tsaftan, ababen bude ido a Afrika, ta kuma gano Akwa Ibom ce tafi zama a tsaftace a fadin a Najeriya.

Kara karanta wannan

Bako cinye gida: Kadan daga tarihin sabon Firayinministan Burtaniya Rishi Sunak

Jihar Akwa Ibom ta fito a jerin jihohi mafi tsafta a nahiyar Afrika
Akwa Ibom Ta Ce Jihar da Ta Fi Kowacce Tsafta a Najeriya, ta Fito a Afrika | Hoto: dailytrust.com
Asali: Facebook

Jihar Akwa Ibom dai ita ce jihar da jama'a da dama suka fi kaunar gudanar da tarukan siyasa, addini, kasuwanci da sauran lamuran yau da kullum.

Wani rahoton Vanguard ta yi tsokaci da cewa, babu mamaki wannan yasa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya zabi jihar domin kaddamar da kamfen dinsa a can.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jiha ce mai albarkatu da ababen more rayuwa, kamar yadda wadanda suka je da kuma rahotanni suka nuna.

Sauran biranen duniya

Sauran jihon da suka fito a jerin sun hada da:

  1. Kigali ta Rwanda
  2. Cape Town ta South Africa
  3. Tunis ta Tunisia
  4. Port Luis ta Mauritius
  5. Johannesburg ta South Africa
  6. Nairobi ta Kenya
  7. Kumasi ta Ghana
  8. Gaborone ta Botswana
  9. Dares Salaam ta Tanzania
  10. Windhoe ta Namibia.

Bana Tsoron Gwamna Mai Ci, Inji Dan Takarar Gwamnan NNPP a Jihar Gombe

Kara karanta wannan

Rundunar Yan Sanda Ta Magantu Kan Yuwuwar Kai Harin Ta'addanci a Najeriya

A wani labarin, dan takarar gwamna a karkashin jam'iyyar NNPP mai kayan marmari a jihar Gombe, Khamisu Mailantarki ya ce sam karfin ikon gwamna Inuwa bai bashi ciwon kai, zai iya lallasa shi a zaben 2023.

Mailantarki ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da wakilin jaridar Leadership, inda yace shi ya saba da tumbuke shugabannin dake kan karagar mulki.

Mai lantarki ya bayyana cewa, kasancewarsa a jam'iyyar NNPP ba yana nufin yana da rauni bane, zai yi iya kokarinsa da ya saba yi wurin samun nasara kan jam'iyyu sanannu a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.