Sarakunan Igbo Sun Afkawa Kotu, Sun Bukaci a Sako Nnamdi Kanu
- Yayin da duniya ta sani, kuma ta dauki kungiyar IPOB a matsayin ta ta'addanci, sarakunan Igbo na ta'allaka kansu da shugabannin kungiyar
- A yau 24 ga watan Oktoba ne wasu sarakunan Igbo suka dura kotu domin fafutukar ganin an sako dan su Nnamdi Kanu
- Kotu ta ce a saki Nnamdi Kanu, amma gwamnatin tarayya ta ce ba za ta sabu ba, domin kuwa akwai sauran batutuwa a kasa
Sarakunan gargajiya shida na kabilar Igbo ne suka dumfaro kotun daukaka kara dake zama a babban birnin tarayya Abuja domin rokon a saki shugaban kungiyar ta'addanci ta IPOB, Nnamdi Kanu.
Sarakunan, dukkansu a cikin sutura ta gargajiya sun ce sun zo ne domin nuna goyon baya ga dansu, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Sun zauna a cikin kotun, sun kuma ji duk yadda aka yi kan bukatar gwamnatin tarayya na ci gaba da tsare Kanu a kalubalantar umarnin kotu na sakinsa.
Jerin sarakunan da suka zo bin kadun Nnamdi Kanu
Sarakunan da suka zauna har aka gama zaman kotu sun hada da;
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- HRM Eze (Sir) Innocent Nwaigwe, sakataren majalisar sarakunan gargajiya na Umuahia ta Arewa
- HRM, Eze Nnamdi Ofoegbu, shugaban majalisar sarakunan gargajiya na Ohuhu
- Eze Iheanyichukwu Ezigbo, shugaban majalisar sarakunan gargajiya na Ibeku
- Eze Pastor Philip Ajomiwe, tsohon shugaban majalisar sarakunan gargajiya na Umuahia ta Arewa
- Eze Eddy Ibeabuchi, tsohon shugaban majalisar sarakunan gargajiya na Umuahia ta Arewa
- Eze Ben Oriaku, na karamar hukumar Ikwuano.
Sai dai, kotu ta tsaya kan hukuncinta game da bukatar gwamnatin tarayya har zuwa lokacin da za a nemi dukkan bangarorin.
Sarakunan Igbo sun sha nuna bacin rai tare da zuwa kotu nuna goyon bayansu ga Nnamdi Kanu.
Yan Sanda Sun Kama Kwamandan IPOB/ESN, Sun Lalata Sansanonin Horar da Tsageru a Ebonyi
A wani labarin, 'yan sandan jihar Ebonyi sun yi nasarar kame wasu mambobin kungiyar nan ta ta'addanci IPOB da sojojinta ESN bayan wani samamen da ta kai kan wasu sansanonin horar da tsageru.
'Yan sandan sun bayyana cewa, wadannan sansanoni na tsageru suna cikin wani duhun daji ne na kauyen Omege a lardin Agba ta karamar hukumar Ishielu ta jihar, The Cable ta ruwaito.
Chris Anyanwu, kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ya kuma bayyana cewa, jami'ai sun kwato makamai da alburusai da kakin sojoji da dai sauran kayayyakin aikata laifi.
Asali: Legit.ng