‘Yan Bindiga Sun Sheke Fasinjoji 2, Sun Yi Garkuwa da Wasu 3 a Katsina
- Miyagun ‘yan bindiga dauke da makamai masu bada mamaki sun kai farmaki kan fasinjoji dake kan babban titin Magamar Jibia a Katsina
- An gano cewa, ‘yan bindigan sun halaka mutane biyu tare da yin garkuwa da wasu ukun yayin da suka tare motoci dauke da fasinjoji
- Tuni tawagar jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sojoji sun kai daukin gaggawa inda suka tarwatsa ‘yan bindigan
Katsina - A daren Asabar ne fasinjoji biyu suka rasa rayukansu inda aka yi garkuwa da wasu ukun bayan tawagar ‘yan bindiga dauke da miyagun makamai suka mai hari iyakar Magamar Jibia dake karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.
Wani ganau wanda ya bukaci a boye sunansa ya sanar da Channels TV a ranar Lahadi cewa ‘yan bindigan sun kai farmakin wurin karfe 9:15 na dare.
Ya bayyana cewa tawagar jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sojoji sun fatattake su bayan tsare ababen hawan biyu da suka yi a babban titin tare da kashe fasinjoji tare da garkuwa da wasu uku.
“Kafin ‘yan sanda da sojoji su fatattake su, sun tsare ababen hawan tare da halaka fasinjojin biyu da kuma garkuwa da wasu ukun. Wannan hoton daya daga cikin wadanda abun ya ritsa dasu ne.”
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
- Majiyar tace.
Duk da jami’an tsaro basu riga da sun tabbatar da lamarin ba, Channels TV ta tattaro cewa duk da raguwar ta’addanci a jihar, Jibia tana daga cikin inda ake fama da harin ‘yan bindiga.
A makon da ya gabata, shugabannin ‘yan bindiga masu yawa sun yada makamai tare da mika wuya ga gwamnatin jihar Katsina domin neman zaman lafiya.
A zantawar da Legit.ng tayi da Malam Salih, mazaunin Magama Jibia kuma ‘dan uwan daya daga cikin fasinjojin da aka yi garkuwa dasu, yace labarin ya zo musu a ba-zata duk da ‘yan ta’addan sun saba kai hare-hare yankin.
Ya sanar da cewa:
”Ana gobe mummunan lamarin zai faru mun hadu da shi har mun gaisa. Muna fara a sako su da tansu. Don yanzu ba biyan kudin fansan bane, sai su halaka wanda suka sace. A taya mu da addu’.”
Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 27 Daga Masu Garkuwa da Mutane
A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ceto mutum 27 da aka yi garkuwa dasu a kauyukan Akawa, Gwashi, Tungar Rogo da Anka wadanda ‘yan bindiga suka kai sansanoninsu na Gando/Bagega da dajikan Sunke a kananan hukumomin Bukkuyum da Anka a jihar.
Jaridar Punch ta rahoto cewa, a yayin jawabi ga manema labarai a ranar Asabar, kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Mohammed Shehu, yace cetonsu ya biyo bayan rahoton da Rundunar ta samu ne kan cewa kungiyar ‘yan ta’addan sun kutsa wasu kauyuka a Anka da Bukkuyum inda suka sace mutane da ba a san yawansu ba.
Asali: Legit.ng