2023: Babban Abin Kunya, Koma Baya Yayin Da Yan Sanda Suka Kama Jigon APC Da PVC Guda 367, An Bayyana Sunansa
- Jigon jam'iyyar APC, Aminu Ali Shana, yana hannun yan sanda bayan an kama shi da katin zabe na PVC 367 a jihar
- An kama Ali ne bayan wasu cikin shugabannin jam'iyyar NNPP a Kano sun tsegunta wa yan sanda da INEC
- Rundunar yan sandan a jihar Kano ta tabbatar da kama Shana ta kuma ce an fara bincike kan lamarin
Kano - Rundunar yan sandan Najeriya reshen Jihar Kano ta kama Aminu Ali Shana, wani jigon jam'iyyar APC bayan an same shi da katin zabe, PVC, a kalla guda 367.
An tattaro cewa jigon na APC shine shugaban jam'iyyar mai mulki a gundumar Yautan Arewa da ke karamar hukumar Gabasawa a jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Laifin da ake zargin Shana da aikatawa ya saba sashi na 21 da 22 karamin sashi na 1 (a), (b) da (c) na dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima.
Yadda aka kama Shana
A cewar The Sun, an kama Shana ne a ranar Juma, 14 ga watan Oktoba bayan kakakin jam'iyyar NNPP a jihar Sanusi Bature ya yi korafi.
Da farko Bature ya yi ikirarin cewa wasu yan siyasa na siya/tara PVC daga hannun masu zabe a wuraren da suke zargin ba dole ne su yi nasara ba a zaben 2023.
Kakakin na NNPP ya kara da cewa shugaban jam'iyyar, Umar Haruna Doguwa, ya umurci sashin shari'a na jam'iyyar su sanar da hukumar INEC da yan sanda don su bincika abin.
Yan sanda sun yi martani
A bangarensu, hedkwatan yan sanda a Bompai sun sanar da jaridar cewa sun fara bincike kan batun, duk da cewa wanda ake zargin ya yi ikirarin jam'iyyar adawa ne suka shirya masa tarko a unguwarsu.
Yan sanda sun mika wa INEC katin na PVC don tattabar da ingancinsu. Ana fatan za a gayyaci masu katin don su amsa tambayoyi.
Da ya ke magana kan lamarin, kakakin yan sandan, Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa an kama Shana kuma ana cigaba da bincike.
Asali: Legit.ng