Da dumi-dumi: Allah Ya Yiwa Dan Sanata David Mark Rasuwa

Da dumi-dumi: Allah Ya Yiwa Dan Sanata David Mark Rasuwa

  • Wani labari mara dadi dake shigowa ya bayyana cewa, Allah ya yiwa dan tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark rasuwa
  • Dan nasa mai suna Tunde Mark, ya rasu ne a birnin Landan bayan wata jinya da ya yi ta cutar daji, inji majiya
  • Ya zuwa yanzu dai ba a dawo dashi Najeriya ba, amma ana kyautata zaton yin bison marigayin a nan gida Najeriya

Landan - A yau muke samun labarin cewa, Allah ya yiwa babban dan Sanata David Mark, Tunde Mark rasuwa.

Wata majiyar dangi mai karfi ta bayyana cewa, Allah ya yiwa Tunde rasuwa ne a ranar Juma'a 21 ga watan Oktoba a asibitin birnin Landan ta Burtaniya.

Allah ya yiwa dan David Mark rasuwa
Da dumi-dumi: Allah ya yiwa dan Sanata David Mark rasuwa | Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Majiyar ta kuma bayyana cewa, ana kyautata zaton cutar daji ce ta kashe Tunde, inji rahoton jaridar Daily Sun.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Tabbatar Da Sherrif Matsayin Sahihin Dan takaran Gwamna

Duk da cewa har yanzu babu cikakkun bayanai game da lamarin ba, an dai ce ana kokarin dauko gawarsa domin biso a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanene Tunde Mark?

Kafin rasuwarsa, Tunde ya kasance tsohon dalibin makarantar sojoji ta Yaba, jihar Legas da kuma makarantar Fernden Prep dake Haslemere a Surrey.

Ya yi digirinsa na farko a Kings College dake Landan. Daga ya wuce ya karanta ilimin halittu a jami'ar Harvard.

Ya rasu ya bar mata daya da da daya, inji rahoton Daily Post.

Wata sanarwar da Paul Mumeh, mai ba Sanata Mark shawari ya fitar a yau Juma'a 21 ga watan Satumba ta tabbatar da rasuwar Tunde, inda ya tabbatar cewa cutar daji ce ta kashe shi.

Sanarwar da jaridar Vanguard tace ta samo ta bayyana cewa, an haifi Tunde ne a ranar 13 ga watan Oktoban 1971.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Muhammadu Buhari Ya Fitittiki Shugaban Hukumar NDDC

Mun Daina Zunubi Domin Dan Takaranmu Atiku Ya Samu Nasara, Inji Dino Melaye

A wani labarin, mai magana da yawun kwamitin kamfen din jam'iyyar PDP a gangamin zaben shugaban kasa na 2023, Sanata Dino Melaye ya bayyana cewa, wasu mambobin majalisar sun daina aikata zunubi saboda nemawa Tiku nasara a zabe mai zuwa.

Melaye ya bayyana hakan ne a wani taro da mambobin jam'iyyar PDP a jihar Kaduna, inda gangamin kamfen din jam'iyyar ya gudana, Daily Trust ta ruwaito.

Ya karanto wasu ayoyin Al-Qur'ani tare da cewa, wasu jiga-jigan PDP sun kame daga aikata zunubu ne domin kwadayin Allah ya amsa addu'arsu idan suka roke shi game da nasarar Atiku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.