Kotun Koli Ta Yanke Hukunci Kan Sahihin Dan Takaran Gwamnan Delta Na PDP
- Bayan watanni ana kai ruwa rana a kotu, daga karshe an raba gardama tsakanin Sheriff da Edevbie
- Kotun koli ta tabbatar da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a makonnin baya
- Yanzu Hanarabul Sherrif Oborevwori na PDP zai kara da Sanata Ovie Omo-Agege na APC a watan Maris 2023
Abuja - Kotu koli ya tabbatar da Kakakin majalisar dokokin jihar Delta, Sherrif Oborevwori, matsayin sahihin dan takaran gwamnan jihar karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Kwamitin Alkalan karkashin jagorancin Amina Augie a ranar Juma'a ya ce hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a baya daidai ne.
David Edevbie, shi ne ya ɗaukaka ƙara zuwa Kotun koli yana mai kalubalantar hukuncin da Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke ranar 29 ga watan Agusta, 2022 a Abuja.
Sheriff Oborevwori ya samu kuri'u 590 yayinda David Edevbie ya samu kuri'u 113.
Yayinda gwamnan jihar Ifeanyi Okowa ke goyon bayan Sheriff, tsohon gwamna James Ibori na goyon bayan Edevbie.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wane hukunci Kotunan baya suka yanke?
A hukuncin da ta yanke, Kotun ɗaukaka ƙara ta sauya hukuncin da babbar kotun tarayya dake zama a Abuja ta yanke, wanda ya soke halascin kakakin majalisar dokokin Delta,Sheriff Oborevwori, a matsayin ɗan takarar PDP.
Oborevwori ne ya zo na farko a zaɓen fidda ɗan takarar gwamnan jihar Delta na jam'iyyar PDP wanda ya gudana ranar 25 ga watan Mayu, 2022.
Sai dai ɗaya daga cikin yan takara, David Edevbie, ya kalubalanci nasarar kakakin majalisar, inda ya yi ikirarin Oborevwori ya miƙa wa jam'iyyar PDP takardun bogi.
A hukuncin ranar 7 ga watan Yuli, 2022, Mai shari'a Taiwo Taiwo na babbar Kotun tarayya ya amince da ikirarin Edevbie kana ya soke zaɓen Oborevwori a matsayin ɗan takarar PDP.
Amma a ranar 29 ga watan Agusta, 2022, Kotun ɗaukaka ƙara da ke zama a birnin tarayya Abuja ta soke hukuncin tare da tabbatar wa Oborevwori da nasararsa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Yanzu Hanarabul Sherrif Oborevwori na PDP zai kara da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege na APC a zaben da zai gudana watan Maris 2023
Asali: Legit.ng