Da Duminsa: Sojoji Sun Ragargaza Fitaccen Shugaban ‘Yan Bindiga Zamfara, Chire
- Zakakuran sojojin Najeriya sun bindige gagararren shugaban ‘yan bindiga, Ibrahim Chire, a wani harin ba-zata da suka kai maboyar miyagun a Zamfara
- Kamar yadda suka bayyana, Ibrahim Chire shine Fitaccen ‘Dan bindigan da ya addabi yankunan Gando, Gwashi, Bukkuyum da Anka da miyagun farmaki
- Hakazalika, an halaka wasu ‘yan bindiga biyu a tare dashi kuma sauran mabiyansa sun arce da raunikan bindiga sakamakon ruwan wutan dakarun
Zamfara - Dakarun sojin Najeriya dake aiki da Rundunar Operation Hadarin Daji sun harbe daya daga cikin gagararren shugabannin ‘yan bindiga na Zamfara.
Daily Trust ta rahoto cewa, kwamandan an gano sunansa Ibrahim Chire wanda ke addabar yankunan Gando, Gwashi, Bukkuyum da Anka.
Daraktan yada labaran tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami a wata takarda da ya fitar a daren Alhamis, yayi bayanin cewa an halaka ‘dan ta’addan ne bayan musayar wutan da suka yi.
Yace biyu daga cikin ‘yan ta’addan an halaka su yayin da mabiyansu suka arce da raunikan bindiga.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Danmadami yayi bayanin cewa:
“Dakarun Operation Hadarin Daji sun yin sintirin har zuwa maboyar ‘yan bindiga dake kauyen Doka a dajin Gando dake karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara a yau 20 ga watan Oktoban 2022.
“A yayin sintirin, dakarun sun ci karo da ‘yan bindiga kuma sun yi musayar wuta. A nan take sojojin suka halaka ‘yan bindiga biyu yayin da sauran suka arce da raunika.
“A yayin duba yankin, daya daga cikin ‘yan bindigan da aka halaka an gano Ibrahim Chire ne, gagararren ‘dan bindigan da ya addabi Gando, Gwashi, Bukkuyum da Anka.”
Ya kara da cewa, dakarun daga bisani sun samo bindiga kirar AK 47, harsasai, babur, wayar salula da sauransu.
Dakarun Sojin Najeriya Sun Dira Maboyar ‘Yan Bindiga Sun Halaka Masu Yawa a Kaduna
A wani labari na daban, a kokarin da dakarun soji suke yi na zuwa har maboyar ‘yan bindiga, sojojin Najeriya karkashin rundunar Operation Whirl Punch sun halaka ‘yan bindiga a wurare daban-daban a wuraren titin Kaduna zuwa Abuja.
Kamar yadda Zagazola Makama ya bayyana, dakarun sun yi aiki kan bayanan sirri inda suka fita sintiri zuwa yankin Abasiya zuwa Amale dake gabashin Polewire a karamar hukumar Kachia inda suka yi wa ‘yan bindigan ruwan wuta.
Asali: Legit.ng