CBN Ta Sayar Da Daya Cikin Shahararrun Bankunan Kasuwanci Na Najeriya, Ta Bayyana Wadanda Suka Siya

CBN Ta Sayar Da Daya Cikin Shahararrun Bankunan Kasuwanci Na Najeriya, Ta Bayyana Wadanda Suka Siya

  • Babban bankin Najeriya ta CBN ta sanar da kammala sayar da daya daga cikin bankin kasuwanci a Najeriya, Bankin Polaris
  • CBN da hukumar kula da kadarori, AMCON, sun jagoranci sayar da Bankin Polaris ne da kamfanin 'Strategic Capital Investment Limited' (SCIL)
  • SCIL ya biya CBN Naira Biliyan 50 a yanzu kuma ya amince da biyan dukkan sauran kudaden da CBN ta kashe don kare bankin daga rushewa

FCT Abuja - Babban bankin Najeriya, CBN, ta sanar da kammala sayar da Bankin Polaris, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Osita Nwanisobi, Direktan sashin hulda da al'umma ne ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar.

Bankin Polaris.
CBN Ta Sayar Da Bankin Polaris. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Surukin Babangida Ne Sabon Mammalakin Bankin Polaris, An Nada MD

CBN ta sanar da sabbin masu bankin

Nwanisobi, ya sanar da cewa CBN da AMCON ne suka jagoranci sayar da bankin ga wadanda suka fi yawan hannun jari a bankin suna 'Strategic Capital Investment Limited' (SCIL), rahoton The Nation.

Sanarwar ta ce SCIL ta biya N50 biliyan nan take don siyan hannun jarin Polaris Bank baki daya kuma ta amince da yarjejeniya da suka hada da biyan N1.305 tiriliyan, da gwamnati ta saka a bankin don ceto shi daga rushewa.

Wani sashi na sanarwar ya ce:

"An biya CBN kudade na daidaito da ta samar a bankin Polaris lokacin da ake kokarin daidaita bankin da tattabar da an samo dukkan kudin da aka bawa bankin lokacin tallafi."
"Wata kwamiti na sayar da kadarori da ta kunshi wakilai daga CBN da AMCON, wacce ta samu shawarwari daga kwarrarru ta jagoranci sayar da bankin. Kwamitin ta sayar da bankin a karkashin tsarin kebabben yarjejeniya 'private treaty' kamar yadda ya ke a sashi na 34(5) na dokar AMCON don gujewa zargi marasa kyau da tabbatar da daraja da kimar sashin hada-hadan kudi.

Kara karanta wannan

Ta karewa tsohuwa minista, kotu ta umarci a kwace sauran kadarorinta dake Abuja

"An gayyaci bangarorin da suka nuna sha'awar suna son siyan Polaris Bank, bayan CBN ta shiga tsakani a 2018 su gabatar da tayinsu. Cikinsu an aika takardar gayyata ga 25, daga cikinsu aka zabi uku don bita kansu.
"An yi nazari da tantance tayinsu inda daga karshe aka zabi SCIL saboda itace ta fi gabatar da sahihin tsari da zai tabbatar da girma da bunkasar Polaris Bank."

Surukin Babangida Ne Sabon Mammalakin Bankin Polaris, An Nada MD

Bayanai sun fara fitowa game da attajirin da ya sayi bankin Polaris Nairan Bilyan 50 a karshen makon da ya gabata.

Sabon mammalakin, Auwal Lawal, suruki ne ga tsohon shugaban kasan mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya).

Ya auri Halima, 'yar autar Janar IBB, rahoton The Nation.

Asali: Legit.ng

Online view pixel