Jerin Sunaye da Kudin da Manyan Attajiran Afrika 5 Suka Tara a Watan Oktoba
- A cikin kwanaki 30 da suka gabata, manyan masu kudi sun ga yadda dukiyoyinsu suka yi kasa ko kuma suka tumbatsa
- A jerin biloniyoyin da Bloomberg suka fitar, manyan attajiran Afrika sun fuskanci cigaba da yalwar dukiyoyinsu
- A cikin jerin attajiran, an ga Aliko Dangote na Najeriya yayi zaman dirshan a matakin farko yayin da ‘yan Afrika ta Kudu suka cika jerin
A kwanaki 30 da suka gabata, Elon Musk, babban attajiran duniya yayi asarar $39 biliyan sakamakon faruwar farashin Tesla.
Har a halin yanzu zaune yake daram a matsayin mutumin da yafi kowa kudi a duniya.
Kamar yadda Bloomberg suka bayyana, manyan attajiran Afrika basu girgiza ba yayin da aka samu sauyi a arzikinsu a watan Oktoban 2022.
Wannan jerin ya duba hawa da saukar arzikinsu da kuma ribar da ake samu a kasuwacinsu wanda yake nuna nawa ake rasawa ko ake samu tun farkon wannan shekarar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aliko Dangote: $18.5bn
Aliko Dangote har yanzu shine zaune daram kuma dirshan a sahun gaba matsayin mutumin da yafi kowa arziki a Afrika inda arzikinsa ya kai $18.5bn.
Ribar da ya samu daga farkon shekarad nan zuwa yanzu ta kai N572 miliyan kuma asarar da ya tafka ta kai $64.4 miliyan.
Johann Rupert da iyalansa: $8.71bn
Iyalan Rupert sune na 206 a jerin biloniyoyin duniya da Bloomberg suka fitar. ‘Yan asalin Afrika ta kudun sun mallaki $8.71 biliyan.
Daga farkon shekarar nan zuwa yanzu sun samu ribar $3.24 biliyan.
Nicky Oppenheimer: $7.93bn
Oppenheimer a yanzu yana da kudi da suka kai $7.93 biliyan. Attajirin mai hakar ma’adanai na kasar Afrika ga kudun yayi asarar $75 miliyan. Daga farkon shekarar nan zuwa yanzu ya samu ribar $25 miliyan kuma yana mataki na 237 na masu kudin duniya.
A watan Yuni, Oppenheimer yafi Rupert da Johann arziki kuma shi ne na biyu a jerin masu kudin Afrika.
Nathan Kirsh: $7.21bn
‘Dan kasuwan asalin ‘dan kasar Afrika ta kudun yana da dukiya da ta kai $7.21 biliyan. Ya samu ribar da ta kai $64.5 miliyan.
Daga farkon shekarar nan zuwa yanzu ya samu $1.06 biliyan kuma yana mataki na 273 na jerin masu kudin duniya. Shi ne na 8 a jerin masu kudin Afrika.
Nassef Sawiris: $6.44bn
Biloniyan ‘dan asalin kasar Misra yana da dukiya mai darajar $6.44 biliyan. A baya bayan nan ya tafka asarar da ta kai $152 miliyan. A yanzu shi ne na 320 cikin mashahuran attajiran duniya.
Asali: Legit.ng