Yadda Yaron Shago Ya Lashe miliyan N16 a Caca a Kasuwar Alaba, Ubangidansa Ya ce Sai Ya Bashi Rabin Kudin
- Wani matashi dan Najeriya ya taki sa'a a kasuwar Alaba da ke jihar Lagas inda ya lashe kudi naira miliyan 16 a caca
- Sai dai yaron ya hadu da cikas domin ubangidansa y ace sai dai su yi raba daidai kowannensu ya kwashi miliyan N8
- Masu amfani da soshiyal midiya sun tofa albarkacin bakunansu yayin da mutane suka bayyana abun da za su yi da sune a matsayin matashin
Lagos - Wani yaron shago a kasuwar Alaba da ke jiharf Lagas ya taki babban sa’a yayin da ya lashe zunzurutun kudi naira miliyan 16 a caca.
A cewar @oku_yungx wanda ya wallafa labarin a Twitter, ya ce ubangidan yaron ya nemi ya bashi rabin kudin da ya lashe.
Mutumin ya bayyana cewa ubangidan ya yi nasara kan yaron domin mutanen kasuwar sun shawo kan yaron a kan ya aikata hakan.
“Wato wannan yaron da ke koyon aiki karkashin ubangidansa a kasuwar Alaba ya lashe naira miliyan 16 a caca kuma ubangidansa ya nemi ya raba kudin gida biyu. Wato ubangidan ya dauki naira miliyan 8.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Na ji cewa mutanen kasuwar sun goyi bayan ubangidan nasa don haka dole ya bi.”
An yi cece-kuce kan yadda lamarin ya kare.
Kalli wallafar a kasa:
Jaa'a sun yi martani
@UnrepentantJ ya ce:
“Ya gode abun ya faru ne a wajen Onitsha lol da ba zai ga ko kwabo ba ubangidan ne zai karbe komai.”
@Ahoysealord ya ce:
“Ina fatan idan lokaci yayi da ubangidan nasa zai sallame shi, ba za a ji tatsuniya ba.”
Yadda Matar Aure Ta Zama Mai Aikin Goge-goge Don Tura Mijinta Makaranta A Kasar Waje, Bidiyon Ya Yadu
@DaCypher ya ce:
“Yawancin mutanen da ke cewa sun yarda, ubangidansa ya yi daidai, da ubangidan ya sani ya karbi dukka, kaza da kaza..na tabbata da sune a matsayin yaron. Da guduwa za su yi da naira miliyan 16 gaba daya.”
Matashi Ya Garzaya Masallaci Bayan Ya Lashe miliyan N38 A Caca Da Ya Buga Da N800, Bidiyon Ya Yadu
A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa wani matashi ya zama miloniya a dare daya bayan ya lashe makudan kudade har naira miliyan 38 a wani gidan buga caca.
Dan Najeriyan wanda ya taki sa'a ya buga cacar na naira 800 kacal.
A wani dan gajeгел bidiyo da @bod_republic ya wallafa a Twitter ya nuno lokacin da labarin gagarumar nasarar da yayi ya karade garin.
Asali: Legit.ng