Gaskiyar Dalilin Da Yasa Aka Tsige Babban Limamin Masallaci A Jihar Ondo

Gaskiyar Dalilin Da Yasa Aka Tsige Babban Limamin Masallaci A Jihar Ondo

  • Takaddama ta shiga tsakanin al'ummar Musulmi a yankin Ikare da ke Ondo da babban limamin masallacin Ikare, Sheikh Abubakar Muhammed Abbas
  • Musulman Ikare sun ce lallai sai dai a nada masu wani limamin daga yankinsu sannan Shehin Malamin ya tafi ya jagoranci al'ummar yankinsa
  • Rikicin ya samo asali ne saboda fitar da Iyometa yankin da limamin ya fito da aka yi daga Ikare tare da nada masu sarkinsu

Ondo - Jaridar The Nation ta rahoto cewa dalilin da yasa al’ummar Musulmi a Ikare suka juyawa babban Limamin Masallacin yankin, Sheikh Abubakar Muhammed Abbas, baya ya bayyana.

A ranar 9 ga watan Oktoba ne Majalisar Musulman Ikare ta sallami Sheikh Abbas wanda ke rike da mukamin Limacin masallacin tun a shekarar 1995.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Taya Minista Pantami Murnar CIka Shekaru 50 A Duniya

Duk da sallamarsa da aka yi, Sheikh Abbas ya jagoranci bayar da Sallar Juma’a da ta gabata cike da tsaro.

Masallaci
Gaskiyar Dalilin Da Yasa Aka Tsige Babban Limamin Masallaci A Jihar Ondo Hoto: The Nation
Asali: UGC

Gwamnan jihar Rotimi Akeredolu wanda ya yi magana ta hannun kwamishinar labarai ta jihar, Misis Bamidele Ademola-Olateju, ya yi umurnin rufe masallacin don zaman lafiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An tattaro cewa Musulman Ikare sun juyawa limamin baya ne saboda daukar Oba Adeleke Adegbite-Adedoyin II, a matsayin Owa-Ale na Iyometa, Ikare, The Nation ta rahoto.

Daga darajar Oba Adegbite -Adedoyin II da aka yi bai yiwa talakawan Olukare na Ikare, Oba Akadiri Saliu Momoh, wanda shine jagoran yankin da masallacin yake dadi ba.

An tattaro cewa Musulman Ikare na adawa da shugabancin Shiekh Abbas kasancewar ya fito ne daga Iyometa Ikare.

Shugaban majalisar Musulman IOkare, Adewale Jimoh, ya ce Olukare da dukkan shugabanni a Ikare sun amince da sallamar Sheikh Abbas.

Kara karanta wannan

Rashin Lafiya Ya Jawo Aka Gaggauta Fita da Atiku Kasar Waje - 'Dan Kwamitin Zaben APC

Adewale ya ce:

“Abun da muke so kawai shine babban limamin ya tafi. Ba zai iya ci gaba da jagoranci a nan ba. Ya koma Iyometa inda gwamnati ta san da wani sarki. Ba zai yiwu ya yi biyayya ga sarakuna biyu ba.
“An tsige shi ne saboda an fitar da Iyometa ne daga Ikare. Shiekh Abbas dan Iyometa ne. ya je chan ya ja mutanensa sallah. Muna so mu samu namu limamin.”

A halin yanzu, matasan Musulmai a Ikare, sun dage cewa za su nuna turjiya ga duk wani yunkuri na tursasa Sheikh Abbass a babban masallacin Ikare.

A waya hira ta wayar tarho, Shehin malamin ya ce zai jira jin umurnin gwamnati kafin ya dauki mataki na gaba.

Wani Gwamna Ya Umurci Dalibai Da Ma’aikatan Gwamnatin Jiharsa Su Fara Sanya Kayan Gargajiya Ranar Juma’a

A wani labarin, gwamnatin jihar Ondo karkashin jagorancin Gwamna Rotimi Akeredolu ta umurci dalibai a makarantun kudi da na gwamnati da su koma sa kayan gargajiya duk ranar Jama’a.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Barke Tsakanin Limami Da Kwamiti: Gwamnan Ondo Ya Rufe Babban Masallacin Jihar

Legit.ng ta tattaro cewa wannan shine matsaya da aka cimma yayin wani taro na majalisar zartarwa a ranar Litinin, 17 ga watan Oktoba.

Hakazalika, an bukaci ma’aikatan gwamnati da su dunga sanya kayan gargajiya a ranar Juma’a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng