'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Basarake da Wasu Mutum Biyu a Sabon Harin Filato
- Yan bindiga sun kashe Magajin Garin Nyalun dake ƙaramar hukumar Wase a jihar Filato, Salisu Idris da daren Litinin
- Maharan waɗan da ake zaton yan fashin daji ne sun kuma kashe wasu mutum biyu kana suka tafi da iyalan Basaraken su Biyar
- Shugaban matasan Wase, Shapi’i Sambo, yace yan bindigan sun sace adadi mai yawa na baburan mutane
Plateau - Wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton yan fashin daji ne sun kashe, Salisu Idris, Dagacin ƙauyen Nyalun, karamar hukumar Wase a jihar Filato ranar Litinin da daddare.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa maharan da ake zargin yan fashin daji ne sun kuma bindige wasu mutum biyu har lahira a ƙauyen.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, mai magana da yawun hukumar yan sandan Filato, DSP Alabo Alfred, yace mutum uku ne suka rasa rayuwarsu.
Yadda yan bindigan suka yi ta'asa
Sai dai a bayanan mazauna kauyen, mutanen uku sun rasa rayukansu ne lokacin da 'yan bindigan suka shiga ƙauyen a kan Babura kuma suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mazauna sun shaida wa wakilin jaridar cewa, maharan waɗan da suka kai farmaki da misalin karfe 8:00 na dare, sun yi awon gaba da mutum 5 ciki har da matan Basaraken biyu.
Shapi’i Sambo, shugaban matasan yankin Wase, ya faɗa wa manema labarai cewa yan bindigan sun sace adadi mai yawa na Baburan mutane yayin harin, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Shugaban matasan ya ce:
"Maharan sun je da yawan gaske kuma suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi ba tare da jinkiri ba. Suka tafi kai tsaye zuwa gidan Mai Anguwa, suka kashe shi sannan suka tafi da iyalansa mutum biyar.
"Sun kuma kashe wasu mutum biyu gabanin su kutsa kai cikin gidan Basaraken gargajiyan."
A wani labarin kuma 'Yan Bindiga Sun Je Har Masallaci, Sun Yi Awon Gaba da Wani Basarake a Jihar Filato
Yan bindiga sun yi awon gaba da Basaraken kauyen Langai, ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato, Umar Mohammad Zarme.
Rahoto ya bayyana cewa maharan sun bi Basaraken har Masallaci lokacin Sallar Isha'i, suka tare shi kana suka yi gaba da shi.
Asali: Legit.ng