Shugaban Jam'iyyar LP Ya Mutu a Hadarin Kaduna, Peter Obi Ya Yi Ta'aziyya
- Shugaban jam'iyyar LP na shiyya a Kaduna, Mallam Lawal Garba, ya rasu a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya
- Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar LP, Peter Obi, ya nuna kaɗuwarsa da jin labarin tare da yi wa iyalansa ta'aziyya
- Ya yi kira ga mambobin LP su tashi tsaye wajen aiki tuƙuru kar su bari shahadar Malam Garba ta tafi a banza
Kaduna - Ɗan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar Labour Party, (LP), Peter Obi, ya shiga yanayin jimami bayan samun labarin rasuwar shugaban jam'iyya na shiyya a Kaduna, Mallam Lawal Garba.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Garba ya rasu ne a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da shi a Titin Kaduna zuwa Zariya yayin da yake hanyar koma wa gida.
Lamarin ya rutsa da shi ne bayan halartar taronsu da manyan arewa wanda ya gudana a Gidan Tarihi watau Arewa Haouse, Kaduna ranar Litinin.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin kwamitin kamfen shugaban kasa na LP, Dr Yunusa Tanko, Mista Obi yace ya yi takaicin jin labarin rasuwar Mallam Garba farat ɗaya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tsohon gwamnan Anambra, Obi, ya ayyana labarin rasuwar Garba da, "Abun bakin ciki da kaɗuwa awa ɗaya kacal bayan mun rabu."
"Ya kasance jagora nagari kuma mai taka muhimmiyar rawa wurin tsare-tsare da aiwatarwa a tawagar kamfe."
"Zuciyata na tare da iyalansa, mambobin jam'iyyar LP, tawagar Obidient, al'ummar yankin Tudun Wada da ɗaukacin mazauna jihar Kaduna."
Marigayin na ɗaya daga cikin jiga-jigan da suka raka Obi da mataimakinsa Baba-Ahmed filin jirgin Kaduna domin koma wa Abuja, a kan hanyar komawa gida ne haɗarin ya yi ajalinsa.
Obi ya ƙara da cewa Jigon jam'iyyar ya yi shahada kasancewar ya rasa rayuwarsa ne a yaƙin ceto Najeriya daga durkushewa.
Bai kamata mu bar shahadarsa ta tafi a banza ba - Obi
Daga karshe, ya yi Addu'ar Allah ya sa ruhinsa ya samu salama kana ya roki mambobin LP su tashi tsaye wajen tabbatar da nasarar baki ɗaya yan takarar LP domin kar rasuwarsa ta tafi a banza.
A wani labarin kuma El-Rufai ya bayyana yadda Peter Obi ya ci mutuncinsa a 2013 saboda ya je Anambra
Gwamnan jihar Kaduna ya tono kadan daga cin zarafin da tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi ya yi masa.
Ya bayyana yadda aka tozarta shi yayin da ya kai ziyarar duba aikin zaben gwamnan da aka yi a jihar Anambra a 2013.
Asali: Legit.ng