Babu Yadda Atiku Da PDP Zasu CI Zabe Idan Na Fita Daga Jam'iyyar, Nyeson Wike

Babu Yadda Atiku Da PDP Zasu CI Zabe Idan Na Fita Daga Jam'iyyar, Nyeson Wike

  • Gwamna Nyesom Wike ya lashi takobin cewa jam'iyyar PDP ba zata iya nasara a 2023 ba tare da shi ba
  • Jam'iyyar PDP dai ta kasance mai lashe dukkan zabukan aka yi Jihar Rivers tun 1999 har yanzu
  • Wike ya sanya kafar wando daya da shugaban uwar jam'iyyar PDP kuma yace ba zasu hakura ba

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Ezenwo Wike, ya bayyana cewa idan ya fita daga jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) yau, babu yadda za'ayi su ci zabe a 2023.

Wike ya bayyana hakan ne yayin hira da yan jarida ranar Juma'a a garin Port Harcourt, babbar birnin jihar.

Yace irin karfin da shi da abokansa ke da shi babu wanda ya isa ya raina su kuma jam'iyyar PDP na bukatarsu idan tana son nasara a 2023.

Kara karanta wannan

Idan Na Tona Asirin Ayu, Ko 'Yayansa Sai Sun Guje Masa: Wike

Wike ya lashi takobin cewa sai shugaban uwar jam'iyyar, Iyorchia Ayu, ya yi murabus daga kujerarsa.

Wikey
Babu Yadda Atiku Da PDP Zasu CI Zabe Idan Na Fita Daga Jam'iyyar, Nyeson Wike

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yace:

"Alkawarin da muka yi kawai shine ba zamu fita daga jam'iyyar ba. Idan muka fita daga jam'iyyar shin ka san irin illan haka?"
"Idan na fita da jam'iyyar yau. Babu yadda za'ayi PDP ta ci zabe. Idan muka fita, zamu fita tare da jama'armu ne, shine gaskiyan magana."
"Shin kana tunanin idan mu gwamnoni biyar muka fita PDP ba zata ruguje ba."

Asali: Legit.ng

Online view pixel