'Yan Kwangilar Magungunan Yaki da Cutar Korona Sun Yi Zanga-Zanga a Abuja
- An samu tsaiko a babban birnin tarayya Abuja yayin da wasu jama'a suka fito zanga-zangar neman hakkinsu a hannun gwamnati
- An samu barkewar annobar Korona a duniya a karshen 2019, lamarin da ya durkusar tattalin arzikin duniya
- Masu zanga-zanga a kofar sakateriyar FCTA sun nuna fushi game da rashin biyansu kudadensu na magani da kayan aikin yaki da Korona
FCT, Abuja - An samu tashin-tashina a birnin tarayya Abuja daga 'yan kwangilar da suka samar magani da kayayyakin yaki da Korona ga hukumar babban birnin tarayya (FCTA) bisa rashin biyansu hakkinsu tun 2019.
Rahoton da muke samu daga jaridar The Nation ya bayyana cewa, 'yan kwangilar na zanga-zanga ne bisa rashin samun cikon kudin da suke bin gwamnati.
An ce 'yan kwangilar sun toshe mashiga ma'aikatar FCT, lamarin da ya jawo cunkoso tare da hana ababen hawa shiga sakateriyar FCTA.
Jaridar 21st Century Chronicle ta ruwaito cewa, mutanen sun zargi sakataren lafiya na hukumar da yin biris dasu da kuma kin basu bahasi game hakkinsu da suka dade suna jira.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Allunan da suke dauki dasu sun nuna kalaman fushi da barranta daga alkawuran da aka dauka musu a baya.
Najeriya ta sha fama da annobar Korona tun bayan barkewar ta a watan Maris din 2020, lamarin da ya daidaita fannonin tattallin arziki da walwala a kasar.
Har yanzu akwai adadin wadanda ke dauke da cutar ta Korona, inji cibiyar kula cututtuka masu harbuwa ta Najeriya (NCDC).
Allah Sai Ya Tambaye Mu Idan Bamu Zabi Dan Takarar APC Tinubu Ba, Inji Kungiyar CAN Ta Legas
A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa, shugabancin kungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen jihar Legas ta bayyana goyon bayanta ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.
Wannan batu na goyon baya na fitowa ne a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba daga bakin shugaban CAN na Legas, Rabaran Stephen Adegbite, inji rahoton jaridar Independent.
A nasa fahimtar, shugaban na CAN ya ce, tabbas Allah zai hukunta duk wani kirista a karkashin CAN ta Legas da ya ki goyon bayan Tinubu a zabe mai zuwa.
Asali: Legit.ng